Gwamnati ta dakatar da harkokin Tiwita a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harkokin kamfanin Tiwita a Nijeriya har sai baba-ta-gani.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Ministan ya nuna yadda ake amfani da shafukan Tiwita wajen aiwatar da harkokin da ke haifar wa Nijeriya cikas.

Kazalika, ya ce Gwamnatin Tarayya ta umarci Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Kasa (NBC) da ta hanzarta shirya shirin bada lasisi ga ɗaukacin OTT da kuma harkokin soshiyal midiya a cikin ƙasa.

Sanarwar ta fito ne ta hannun hadimi na musamman ga Shugaban Ƙasa kan sha’nin yaɗa labarai Mr Segun Adeyemi, daga ofishin minista.

Idan dai za a iya tunawa, cikin wannan makon ne Tiwita ta goge wani saƙon da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na twita bisa cewa shugaban ya saɓa mata ƙa’ida.