Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse
Gwamnatin Jihar jigawa tace za ta Gina banɗakuna a kasuwanni da tashohin mota, a ƙoƙarinta na yaƙi da ba-haya a bainar jama’a da wasu ke yi.
Kwamashinan ruwa na jihar, Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa ya bayyana haka a wajen bikin ranar tsafta da wanke hannu ta duniya da ya gudana a makarantar kiwon lafiya ta Jahun.
Kakakin Majalisar dokokin jihar Alh. Haruna Aliyu Ɗan Gyatin ya wakilci Gwamna Umar Namadi a yayin taron ƙaddamar da banɗakuna da Hukumar Albarkatun Ruwa ta gina a makarantar.
Hannun Giwa ya ce irin waɗannan banɗakuna, gwamnati ta samar da guda 35 a wasu manyan makarantun jihar a ƙoƙarin tare da hukumar da nufin inganta yanayin tsaftar muhalli.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ita ce ta ɗaya a Nijeriya wajen hana yin ba-haya a bainar jama’a.
Ya kuma ce tuni gwamnatin ta ɗauki matakan hana yin ba-haya barkatai a faɗin jihar ciki har da kasuwanni da tashoshin mota, sannan sunan sa ran nan da wata biyu, doka za ta fara aiki masu irin wannan aiki na ɓata muhalli.