Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Zamfara ta Yamma, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar, ya bayyana aniyarsa ta samar da ababen more rayuwa ga al’ummar mazaɓarsa da nufin rage zaman banza musamman a tsakanin matasa.
Sanata Yari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji), Shugaban kwamitin yaɗa labaransa na ƙungiyar siyasa, ya fitar a ranar Asabar.
Ya ce, “Hakan zai taimaka matuƙa wajen hana su shiga wasu munanan ɗabi’u dake haifar da ƙara tabarbarewar tsaro a cikin al’umma.”
Sanarwar ta bayyana cewa, Sanatan ya faɗi haka ne a wajen bikin yaye sojoji karo na 87 da aka gudanar a Defot na Sojojin Najeriya dake Zariya a Jihar Kaduna.
Sanatan wanda ya samu wakilcin kodinetan shiyyar mazaɓar Zamfara ta Yamma, Talata Mafara, Alhaji Sha’ayau Yusuf (Ɗanmalikin Mafara), ya tunatar da Sojojin da aka yaye da suyi la’akari da matsalolin tsaro da ake fuskanta a ƙasar.
Ya ce zaman banza a tsakanin matasa shi ne abin da ya dame shi, kuma hakan ne ya sa zai cigaba da samar da hanyoyin taimaka musu ko ta halin ƙaƙa.
Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, ya shawarci sabbin sojojin da a ɗauka su 74 da suka fito daga mazaɓarsa da su ɗauki shiga aikin sojan Nijeriya a matsayin kira ga aikin taimaka wa ƙasa, ya na mai cewa su yi ƙoƙarin nuna kishin ƙasa da jarumtaka yayin aikinsu.
A baya ne Sanatan ya bayar da damar ɗaukar matasa 84 da suka fito daga ƙananan hukumomi shida da suka haɗa da; Talata Mafara da Bakura da Bukkuyum da Anka da Gummi da kuma Maradun aikin soja.