Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamitin almajirai

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamitin da zai duba tsarin karatun Almajirai tare da ɓullo da hanyar da za a inganta ilimin da jin daɗin su.

Sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari ya ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnan jihar Malam Dikko Raɗɗa.

Ya bayyana kudirin gwamnatin jihar na inganta ilmi, musamman ta hanyar daidaita karatun Almajirai da na zamani.

Barista Faskari ya buƙaci kwamitin ya mayar da hankali wajen yadda za a daidai tsarin karatun Almajirai da na zamani.

A jawabinsa shugaban kwamitin, Furofesa Abdulhamid Ahmed wanda kuma kwamishinan ma’aikatan cigaban karkara da zamantakewa, ya tabbatar da cewa za suyi iyaka ƙoƙarin su wajan cimma manufofin da gwamnati ta sa a gaba.

Yayi alƙawarin cewa kwamitin zai iya bakin ƙoƙarin sa na ganin sun kammala aikin da aka basu kan lokaci, musamman ganin yadda gwamnati ta ɗauki shirin da muhimmanci.

Ana sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari yadda za a inganta tsarin ilimin Almajirai tare da daidaita shi da buƙatar zamani.