Zelensky ya ruga Saudiyya don sulhu

Kamar yanda a ka yi hasashe cewa lokaci ya yi ga shugaban Yukrain ɓolodymyr Zelensky ya mika wuya don kawo ƙarshen yaƙin da ƙasar sa ke yi da Rasha, ya zama dahir don yadda lamura yanzu su ka bayyana ƙarara. Hakika akwai lokacin cizo akwai kuma na yakushi sannan ƙarshe akwai na harara a duhu. Ba dadi ko kaɗan a ce duniya ta zama fage ne da kullum manyan labaru su ne yake-yake da zubar da jini. Cacar baki da nuna fin ƙarfi daga ƙasashe masu takama da makaman ƙare dangi kan raunanan ƙasashe. Ai mun sha gwada misalin yadda gaggan ƙasashe ke maida wasu ƙasashen su zama fagen yaki inda wannan ƙasar ta ke mara baya ga gwamnati waccar ga ‘yan gwagwarmaya ko tawaye. Ko Sham wato Siriya kafin faɗuwar mulkin Bashar Al’Asad haka ta kasance fagen kare muradu tsakanin Amurka da Rasha. Ga Yaman inda Iran ke marawa gwamnatin da ta kasance ta ‘yan tawaye wato Houthi a gefe guda yayin da Saudiyya ke neman dawo da zaɓaɓɓiyar gwamnatin ƙasar. Har yau Houthi ke mulkin babban birnin ƙasar San’a’a da tashar jirgin ruwa ta Hodeida yayin da gwamnatin ƙasar ke can birnin Aden na kudanci. Hatta ma ai Gaza kan ta a irin wannan yanayin ta ke inda Isra’ila ke da goyon bayan gaggan ƙasashe su kuma ‘yan gwagwarmaya ko mayakan Hamas ke samun goyon bayan wasu ƙungiyoyin ketare musamman Hezbollah a Lebanon. Isra’ila za ta tayar da jiragen yaƙi ta tinkari Gaza inda ‘yan Hamas ke riƙe jifa da majajjawa da sauran makaman harbi-ka-ruga ko bin ramukan ƙarƙashin ƙasa don zama kauda bara. Ba ta yanda za a yi in ba don tsananin kishin ƙasa ba a ce Hamas ta yi wuni biyu kacal ta na yaƙi da Isra’ila. Ga fitinar Sudan tsakanin shugaban gwamnatin soja Abdelfatah Burhan da na sojojin sa kai Hameti Hamdan Daglo; har yau Sudan ba ta samu zaman lafiya ba. Kai mu ma dawo Nijeriya shin wa ke ɗaukar nauyin ta’addanci ne a ƙasar? Akwai nazarin da zai tabbatar ma na masu kai hare-hare na samun makamai ne daga hannun makera na cikin gida?

Abun akwai ban mamaki don fitinar arewa maso gabar ta faro ne tun 2009 amma har yau sai ka ji an kai hari ƙauye kaza ko an yanka manoma kamar raguna. Arewa maso yamma baya ga barayin daji ga wata ƙungiya ta Lakurawa da a ka ba da labari asali daga Mali ta samo asali na aikata aiyukan da su ke keta haddin jama’a.

Arewa ta tsakiya ma ai an sha samun masu son dasa kiyaiya da zummar kawo fitinar addini ko ƙabilanci. In ma can kudu maso kudu an samu sassaucin tsageran Neja Delta ai kudu maso gabar har yanzu na fama da ‘yan tawayen Biyafara na IPOB da kan kashe mutane farar hula da jami’an tsaro. Miyagun ma kan sace mutane don aikata ta’addanci. ‘Yan aware na ganin za su iya cimma wannan burin ta fito na fito da zubar da jini. Rashin ɗaukar darasi daga yaƙin basasar Nijeriya ya zama abun takaici ga waɗannan mutane da ke kawo azabar rayuwa har ma ga jama’ar da su ke son mulka har dai za su samu ƙirƙiro wannan ƙasa. Mun tuna lokacin yaƙin basasa ai an samu wata babbar ƙasar ƙetare na mara baya ga madugun ‘yan tawaye Odumegwu Ojukwu don wargaza Nijeriya a kafa Biyafara.

Can ma kudu maso yamman ai na da tarihin fitina don har gobe zai yi wuya ka shiga Lagos ka kwan biyu ba ka ga gawa a kan titi ba. ‘Yan rajin kafa ƙasar Oduduwa na nan a bayan fage da tada muryar su a duk lokacin da su ka ga buƙatar hakan ta taso. Ran ɗan adam musamman a ƙasashe masu tasowa bai da daraja sosai a wasu ƙasashen ma ai kamar na kiyashi ne.  A nan ma za mu iya tunawa da yanda ta kaya a Rwanda tsakanin Hutu da Tutsi inda a ka zayyana ƙabila guda wato Tutsi da zama kamar kyankyasai ko ran kyankyaso don haka in an kashe dan ƙabilar duk bai fi kamar mutum ya shiga banɗaki ya ga kyankyaso ya sanya kafa ya murje shi ba. Duk irin wannan fassarar ta raina ran ɗan adam a ke gudu daga mugayen mutanen da ko cinnaka ba za su iya halitta ba!. Laberiya an zubar da jini bayan kashe marigayi shugaba Samuel Doe wanda a ka fille kan sa inda su ma a Saliyo ba su tsira daga kisa ba da ta’addancin yanke gabban mutane hatta jarirai don baƙar zuciya da rashin alƙibla. Don haka ya dace duk hanyar da jama’a za su bi wajen rufe kofar fitina to su yi hakan don gaskiyar magana in fitina ta taso ta kan rutsa da wanda ko fitowa daga gidan sa bai yi ba.

Mun koma kan babban darasin mu na Yukrain inda Shugaban Yukrain ɓolodymyr Zelenskyy ya sauka a Saudiyya don gabanin ganawar da wakilan Amurka su ka yi da manyan jami’an gwanatin sa a Talatar da ta gabata.
Yarima Muhammad bin Salman ya karɓi Zelensky da ƙarfafa manufar Saudiyya ta bin duk matakan duniya wajen kawo ƙarshen yakin Yukrain da Rasha.

Da alamu taron zai ba wa Zelenskyy damar sulhu da Amurka bayan cacar bakin da ya yi da shugaba Trump a fadar White House har Amurka ta zaiyana shi da marar da’a ko mai ɗaukar matakan rashin sanin ya kamata.

Tuni shi ma sakataren wajen Amurka Rubio Marco ya isa Jedda inda ya wakilci Amurka a ganawar da ta haifar da sakamako mai ma’ana.
Ba mamaki taron ya samar da hanyoyin maslahar kawo karshen yaƙin mamayar Yukrain da Rasha ke yi bayan janye goyon bayan Yukrain da Amurka ta yi.

Wannan rashin mamakin kuwa shi ya tabbata don an cimma yarjejeniya da wakilan Yukrain na tsagaita yaki da Rasha na tsawon wata ɗaya. Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya halarci taron don zama shaida kulla wannan yarjejeniya mai muhimmanci. Sakataren wajen Amurka Marco Rubio ya nuna yanzu abun da ya saura a mika kofin yarjejeniyar ga fadar Kremlin don dubawa da ɗaukar matakin da ya dace. A nan Amurka ta janye matakin da ta ɗauka na daina musayar bayanan sirri da kuma dakatar da tallafawa Yukrain da makamai. Haƙiƙa wannan na nuna ƙarfin Amurka kan muradun ta a Yukrain don a tsohuwar gwamnatin Joe Biden ta mara baya ne ga shugaba Zelensky inda dawowar Donald Trump lamura su ka canja. Duk da mara baya da ƙasashen turai su ka yi wa Zelensky da alwashin cigaba da ba shi tallafi bayan cacar baki da ya yi a Fadar White House hakan bai sa ya dogara ga ƙasashen ba don yadda ya garzaya Saudiyya ya kai caffan ban girma don yadda ƙasar ta Larabawa ta zama bigiren da za a samu maslaha. Da muguwar rawa gwara kin tashi don goyon bayan Amurka ne ya sa Zelensky ya kai har wannan lokaci ya na karakaina a tsakanin ƙasashe da furta kalaman da ya ga dama na turjiya ga Rasha. Yanzu dai ya fahimci da bazar Amurka ya ke rawa. Irin goyon bayan da ya samu a gwamnatin Biden ya wuce don salon Trump ya sha bamban kan yaƙin.
Gabanin wannan taron na Yukrain shi ma shugaban Lebanon Joseph Aoun ya ziyarci Saudiyya don samun goyon bayan ƙasashen da ke da muhimmanci. Wannan ne ziyara ta farko da Aoun ya kai ketare tun hawa karagar mulki a watan Janairu. Hakan ya zama damar sake raya tattalin arzikin Lebanon da farfaɗo da ƙasar bayan hare-hare da Isra’ila ta riƙa kai wa ƙasar. Matsalar ƙasar ma ta fara da gagarumar asara a sanadiyyar fashewar makamai a tashar jiragen ruwa ta ƙasar.

Lebanon ta buƙaci Isra’ila da ta janye dukkan sojojin ta daga yankin ƙasar ta bayan cimma yarjejeniyar daina kai hare-hare da Isra’ila ke yi da sunan yaƙi da Hezbollah.

Firaministan Lebanon Nawaf Salam ya buƙaci janyewar yayin da ya kai ziyara kudancin Lebanon ɗin don duba yanda Isra’ila ta janye amma ta cigaba da zama a wasu tsaunuka 7.
Salam ya ce lallai Isra’ila ta janye dukkan sojojin ta da kuma tabbacin al’ummar Lebanon za su iya komawa lami lafiya gidajen su a kudanci da fara aikin sake gina yankin.

Hakanan Salam ya ce sojojin Lebanon ke da cikekken haƙƙin kare ‘yancin ƙasar da al’ummar ta.

Kammalawa;

Duk tsawon fitina ko yaƙi ya zama wajibi a hau teburin shawari don samun maslaha. Kun ga duk yanda yaƙin Yukrain ya hargitsa kasar ba da cimma nasarar shiga NATO ba amma ya zama sai da a ka shigo Jeddah a ka tattauna kuma nan ma sai fadar Putin ta Kremlin ta amince sannan za a kammala rantaba hannu kan yarjejeniyar. Zama lafiya ya fi zama dan Sarki. Darasi ne ga dukkan ƙasashe su san cewa ba ribar barin bangon su ya tsage har ƙadangare ya samu wajen fakewa. Hakanan su ma manyan ƙasashen duniya su san cewa lokaci ya yi da za su daina mara baya ga yaƙi a matsayin hanyar nuna ƙarfi ko izzar su a duniya.