Daga AISHA ASAS
TAMBAYA: Mene ne hukuncin ma’auratan da suka yi mu’amalar aure a lokacin da suke ɗauke da azumin Ramadan?
AMSA: Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a wannan darasi a ƙarƙashin shafin Iyali. Allah Ya karɓi ibadunmu ya sa mu dace da samun aljanna. Kamar yadda muka yada zango a tambayar da a wannan satin za mu amsa ta. Ba ya halasta kusantar iyali a lokacin da ake ɗauke da azumi kowane iri, ma’ana na Ramadan ko na nafila.
Hukuncinsa na shiga babin ci da sha yayin azumi, ko jinin haila da jinin haihuwa. Saidai ba za mu iya cewa hukuncinsu ɗaya ba ne, kamar yadda malaman fiƙihu suka bayyana.
Za ka iya ci ko sha bisa babin lalura ta ciwo, ko tafiya mai tsawo, wanda ya halasta yin hakan a Musulunci. Kuma babu ta inda jinin haila ko na haihuwa zuwansa zai zama ganganci ko haifar da fushin Allah. Saɓanin kusantar iyali a cikin azumi, wanda wasu malamai ke ganin babu ta inda za a yi hakan ba bisa ganganci ba, ma’ana a duk lokacin da hakan ta kasance, tabbas kaffara ta hau kan waɗanda suka aikata. Duk da cewa wasu na ganin akwai yiwar aikatawa bisa mantuwa, ma’ana matar ta manta tana azumi, shi ma mijin ya manta har sai da suka gama, idan hakan ta kasance, to za su kama baki, sannan su rama ɗaya bayan wucewar Ramadan.
Yayin da wasu ke ganin ba ta yadda ma’aurata za su iya mantawa a tare, ba tare da ɗaya ya tuna ba har ya tunatar ba. Ala kulli halin dai Allah da zuciya yake amfani. Don haka babu mai iya yanke wannan hukunci sai shi bawan da ya aikata da kuma Mahaliccinshi.
Idan mun dawo kan amsa wannan tambayar, wanda ya kusanci iyalinsa alhali yana ɗauke da azumin Ramadan, to kamar wanda ya ci ko ya sha da gangan ne a hukunci, wato azumi sittin, ko ciyar da miskinai sittin, ko ‘yanta bawa guda.
Tambaya ta farko ita ce, shin mijin ne kawai zai yi sittin ko har da matar? Ya zo a cikin wata ƙissa da ta wakana a zamanin manzon rahma (SAW), a wata rana, wani ya zo wurin Manzon Allah, hankalinshi a tashi, ya ce, “Ya rasulullah, haƙiƙa ni na kusanci iyalina alhali ina ɗauke da azumin Ramadan.” Sai Manzon rahma ya ce, ya je ya yi azumi sittin, sai ya ce, a talatin ɗin ma ya kasa jurewa, ina zai iya jure sittin. Sai Manzo ya ce, ya je ya ciyar da mabuƙata sittin. Sai ya ce, daƙyar ma yake ciyar da kansa da iyalansa. Sai Annabi ba shi abincin da zai isa ciyar da mabuƙata sittin ya ce, ya je ya ciyar (ma’ana, Annabi ya sauke masa wannan kaffara ta hanyar ba shi abinda zai ciyar), Sai wannan bawan Allah ya ce wa Manzon rahma, ba ya jin akwai wani mabuƙaci da ya kai sa, sai Annabin Allah ya yi murmushi, kafin ya ba shi umurnin ya ɗau abincin ya je ya ciyar da iyalinsa.
Da wannan ne wasu malamai suke ganin miji ne kawai kaffara ta hau kansa a yayin da ya kusanci matarshi. Saidai tambayar anan, Shin idan matar ce ta ja ra’ayin mijin zuwa aikata hakan fa?
Shin hakan na nufin talaka zai kuɓuta daga kaffara bayan aikata irin wannan ɓarnar?
Mu kasance a sati na gaba, don samun amsoshin waɗannan tambayoyin da kuma ƙarin bayani kan darasin namu.