Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta wasu rahotanni dake cewa ta yi zaman sulhu da ‘yan bindinga a ƙaramar hukumar Batsari, ɗaya daga cikin ƙananan hukumonin da ‘yan bindingar suka fi kai hare hare a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Dakta Bala Salisu ne ya bayyana hakan.
Kwamishinan ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin Jihar Katsina na nan kan bakanta na ƙin sasantawa ko yin wani zama na sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan bindingar.
Sai dai Dakta Salisu, ya nanata aniyar gwamnati na karɓar duk wani ɗan bindiga da ya nuna zai miƙa wuya ga jami’an tsaro ya kuma yadda zai ajiye makamansa don samun zaman lafiya.
“Ba mu shiga cikin wata yarjejeniya ta zaman lafiya ba, kuma matsayin gwamnati a ko yaushe shi ne cewa duk wanda ya yi watsi da tashin hankali ya miƙa makamansa za a duba lamarinsa. Amma gwamnati ba za ta je neman tattaunawa da duk wani ɗan bindiga ba” In ji majiyar Daily Trust.
Blueprint Manhaja ta samu rahotanni dake nuna cewa an gudanar da wani taron zaman sulhu tsakanin wasu shugabannin ‘yan bindinga da wakilan sojoji da jami’an tsaron DSS da sarakunan gargajiya da kuma mazauna wasu ƙauyuka dake ƙaramar hukumar Batsari a ranar Lahadi.
Saboda haka ne ake yaɗa cewar gwamnatin jihar Katsina ta yi zaman sulhu da shugabannin ‘yan bindingar inda suka miƙa makamansu ga jami’an tsaro, sai dai jami’an tsaron soji sun bayyana cewa zaman da aka yi da ‘yan bindingar ba zaman sulhu bane, hare haren sojoji akan dabar ‘yan bindingar ne ya tilasta masu miƙa wuya ga jami’an tsaro.
Wani mazaunin yankin da ya yi iƙirarin halartar tattaunawar ya ce, “’yan bindigar na son komawa cikin al’ummarmu don su zauna da mutane lafiya, sun yi alƙawarin kawo ƙarshen hare-haren da suke kai wa.
Sun miƙa makamansu tare da sakin waɗanda suka yi garkuwa da su, suna masu ikirarin cewa wannan shi ne mafarin shirin samar da zaman lafiya.”
Rahotanni sun ce manyan ‘yan bindigar da suka haɗa da Lamu Saudo, Abdulhamid Ɗan ɗa, Umar Black, da Abu Raɗɗa, sun miƙa makamansu tare da sakin waɗanda suke tsare da su.
Laftanar Lawal, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 17, ya tabbatar da miƙa wuya da ‘yan bindingar suka yi, yana mai alaƙanta wannan cigaba da matsin lambar da ‘yan bindingar ke fuskanta daga jami’an tsaro.