Gwamnatin Kaduna ta ware Naira biliyan 3.8 domin biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ba da umarnin bai wa hukumar fansho ta jihar Naira biliyan 3.8 domin gaggauta biyan kuɗin giratuti da na haƙƙoƙin ma’aikatan da suka mutu da duk wani abu da ya kamata a bayar.

Wannan umarni na zuwa ne bayan roƙo da tsofaffin ma’aikata da iyalansu suka yi kan ma’aikata da suka rasu suna masu ƙorafin cewa shirin tantancewar da ake yi ya jefa rayuwarsu cikin wani mummunan hali.

Gwamna Uba, a lokacin da yake yin ƙarin haske kan tantancewar da ake yi, ya ce, muhimmancin shirin shi ne gano ‘yan fansho na bogi da aka shigar da su tsarin biyan kuɗin. Sai dai ya bai wa hukumar fansho umarnin gaggauta fara biyan ‘yan fanshon haƙƙoƙinsu.

Gwamnan ya ba da tabbaci ga ‘yan fanshon cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen kula da walawalarsu wanda hakan ne ma ya sa shi ƙoƙarin tantancewa saboda a riƙa biyan fanshon duk wata ba tare da wata tangarɗa ba.

Gwamnan ya ce tilas ne a biya ma’aikatan da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimta wa jihar Kaduna, kuma lallai ne mu ba su dukkan tallafin da ya kamata domin samun farin ciki a yayin da suke lokacinsu na ritaya.

Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa za a ƙara sauri wajen tantancewar ta yadda ‘yan fansho a jihar Kaduna za su mori tsarin biyan su kuɗi ba tare da katsewa ba.

Daga nan ne ya gode wa ‘yan fanshon saboda irin haƙuri da uzuri da cigaba da mara wa gwamnatinsa baya da suke yi.

Ya ce tun bayan shigarsu ofishin gwamna a watan Mayun 2023, Uba Sani ya biya garatuti da haƙƙoƙin ma’aikatan da suka mutu sa sauran haƙƙoƙi da suka kai Naira biliyan 6.6.

By ukarofi