Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi a manyan makarantu

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta haɗa kai da manyan makarantun gaba da sakandare domin faɗaɗa shirin dasa bishiyoyi da inganta kiyaye muhalli a faɗin jihar.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya ƙaddamar da shirin a Kwalejin Musulunci da Ilimin Shari’a ta Mallam Aminu Kano, wato Legal, inda mahukuntan makarantar da wakilan ɗalibai suka nuna goyon bayansu ga shirin.

Sun kuma yi alƙawarin kula da bishiyoyin da aka dasa tare da tabbatar da an kare su daga lalacewa.

A ƙarƙashin shirin, za a bai wa kowace bishiyar da aka dasa lambar tantancewa ta musamman, sannan a ware wasu daga cikin jami’an makarantar domin kula da bishiyoyin, bibiyar yadda suke girma da kuma tabbatar da an kare su.

Kwamishinan ya ce shirin wani ɓangare ne na babban shirin dashen bishiyoyi da gwamnatin Jihar Kano ke aiwatarwa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya bayyana cewa gwamnatin ta taɓa aiwatar da shirye-shiryen dasa bishiyoyi miliyan ɗaya da kuma miliyan uku, yayin da a yanzu take ƙara faɗaɗa shirin zuwa babban buri na dasa bishiyoyi miliyan 10 a wannan shekara.

Dakta Dahiru Hashim ya bayyana dasa bishiyoyi a matsayin saka hannun jari na dogon lokaci mai fa’ida ga muhalli, domin bishiyoyi na taimakawa wajen tsaftace iska, rage zafin yanayi, yaƙi da zaizayar ƙasa, samar da inuwa da kuma kare halittun da ke rayuwa a cikin muhalli.

Kwamishinan ya kuma ƙarfafa gwiwar ɗalibai da su zama jakadun kare muhalli ta hanyar shiga ayyukan dasa bishiyoyi, kula da wuraren renon tsirrai da kuma kare bishiyoyin da aka dasa.

A yayin taron, wakilan makarantar sun gabatar wa kwamishinan wasu buƙatu na gaggawa, ciki har da samar da ingantaccen ruwan sha a makarantar.

Sun ce samun isasshen ruwa na da matuƙar muhimmanci wajen tsafta, kiwon lafiya da kuma ayyukan lambu da ake gudanarwa a makarantar, musamman ganin yadda ɗalibai ke samun horo kan aikace-aikacen noma.

Makarantar ta kuma nemi taimakon gwamnati wajen samar da katafaren ɗakin noman zamani, wato greenhouse, domin inganta koyar da aikin gona, gudanar da bincike da kuma noman amfanin gona ta hanyoyin da suka dace da sauyin yanayi.

By ukarofi

Leave a Reply