Gwamnatin Katsina ta fara ɗaukar matakan kariya daga ambaliya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta fara shiri domin kauce wa samun ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomi bakwai da ke jihar .

Hakan ya biyo bayan hasashen da Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NIMET ta yi game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohi.

Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba Faskari ya faɗi haka a yayin da ya ke ganawa da masu-ruwa-da-tsaki akan kula da sauyin yanayi a Katsina.

Ya ce, taron zai nemo hanyar da za a ankarar da waɗannan ƙanana hukumomi da aka yi hasashe akai.

Ƙananan hukumomin kuwa sun haɗa da; Katsina, Kaita, Bakori, Bindawa, Faskari da kuma Daura, kamar yadda sakataren gwamnatin ya bayyana.

Abdullahi Faskari ya ce, akwai buƙatar a wayar da kan waɗannan ƙananan hukumomi akan haɗarin da ke tafe kamar yadda NIMET ta yi hasashe.

Don haka ya yi kira ga ƙananan hukumomin da su ɗauki matakai na gaggawa na kauce wa afkuwar iftila’in.

By Babaji