An gudanar da musabaƙar Al-Ƙur’ani a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An kammala Musabaƙar karatun Ƙur’ani a masallacin Bani comassie da ke cikin garin Katsina, ƙarƙashin shugabancin limamin masallacin, Sheikh Sama Adamu Bakori.

Shugaban kwamitin shirya Musabaƙar ya ce, yara 20 da suka fito a makarantun Islamiyya da na karatun Allo da na boko ne suka shiga gasar.

Ya ce, ɗalibai goma ne suka samu nasarar lashe gasar karatun Al-Ƙur’anin.

Ya kuma yi godiya ga shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar kuma lamiɗon Katsina, Alhaji Jabiru Salisu tsauri wanda ya ɗauki nauyin Musabaƙar.

Sheikh Sama Bakori ya bayyana lamiɗon a matsayin mutumin kirki da ke ƙoƙarin taimaka wa al’umma da addinin musulunci.

Sai yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da Alhaji Tsauri wajen ɗaukar nauyin ire-iren waɗannan gasar da taimakawa mabuƙata.

Shugaban Musabuƙar ya kuma yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa bisa ƙirƙiro hukumar Hisbah da kuma hukumar Zakka da waƙafi a jihar waɗanda ce gaba ne wajen tsarkake al’umma da ciyar da mabuƙata.

By Babaji