Gwamnatin Katsina ta tallafa wa iyalan ‘yan sanda da suka mutu da Naira Miliyan 3.5

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Katsina ta tallafawa iyalan ‘yan sandan da suka rasa rayukansu wajan yaƙi da ‘yan ta’adda a jihar.

Da yake miƙa kuɗaɗen ga iyalan mamatan, muƙaddashi kwamishinan ‘yan sanda a jihar DCP Aminu Usman Gusau ya jajantawa iyalan ‘yan sandan da bayyana su a matsayin jajirtattu.

Ya ce sun sadaukar da rayukan su wajan bautawa ƙasa a sa’ilin da suke fagen fama .

Muƙaddashin kwamishinan ya ƙara da cewa wannan tallafin kuɗin ba zai biya irin sadaukar da kai da suka yi ba wajen kare lafiyar al’ummar jihar Katsina.

Sai ya yaba gwamnatin malam Dikko Raɗɗa irin kulawa da yake bawa jami’an tsaro a jihar.

DCP Usman Gusau ya jinjina wa gwamnan wajan yaƙi da ta’addanci a jihar.

Iyalan yan sandan guda 7 da suka rasa rayukansu kowannen su ya sami N500.000.

Daga ƙarshe yayi fatan Allah raya abinda suka bari.

By ukarofi