
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rushe kantomomin riƙon ƙwarya na gudanarwar ƙananan hukumomin jihar 44.
Hukuncin ya fara aiki ne nan-da-nan wanda aka sanar a zama na tantancewa da mambobin kwamitocin a Fadar gwamnatin jihar.
Wata takarda da Kakakin gwamnan, Sanusi Tofa ya fitar, ta ce hakan na nufin kawo ƙarshen watanni shida na kantomomin waɗanda a lokacinsu suka yi aiki da gwamnatin jihar musamman wajen zartar da tsare-tsarenta na tushe da kuma shirye-shirye.
Gwamna Abba ya yaba wa mambobin kwamitocin kan saduakarwarsu da ƙoƙari da suka yi wa harkokin ƙananan hukumomin, ya na mai cewa sun taka muhimmiyar rawa ga ƙoƙarin gwamnatinsa na samar da cigaba daga tushe.
Ya tabbatar musu da cewa, ba za a watsar da su ba a yayin gudanar da harkokin gwamnatinsa inda ya ce za a ke damawa da su don amfanin al’ummar jihar.
Abba ya kuma umarci a miƙa harkokin gudanarwar ƙananan hukumomin ga Daraktocin gudanarwa na Ma’aikata (DPMs) na kowacce ƙaramar hukuma.
Daraktocin za su yi aiki ne a matsayin masu sa-ido har zuwa lokacin zaɓen ƙananan hukumomin wanda za a yi a ranar 24 ga watan Oktoba, 2024.
Gwamnan ya yi kira gare su da su tabbatar da gaskiya da adalci yayin gudanar da ayyukansu.
Rushe kwamitocin na zuwa ne a yayin cigaba da shirye-shiryen zaɓukan ƙananan hukumomin wanda za a yi a wata na gaba.
