
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba zai samu halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 ba na wannan shekarar wanda za a yi a New York, yayin da ya umarci Mataimakinsa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Nijeriya a yayin tafiyar.
Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya faɗi hakan cikin wata takarda da fitar inda ya ce kasancewar a makon da ya gabata, Tinubu ya dawo daga ƙasar Chana, ya sa ba zai samu zuwa taron ba, madadin haka, zai mayar da hankali kan al’amura na cikin gida da suka damu al’umma musamman aukuwar ambaliyar ruwan sama a ƴan kwanakin nan a wasu sassan Nijeriya.
Ya ce, Shettima shi ne wanda zai gabatar da jawabin Nijeriya a madadin Tinubu a taron da zuwa wasu tarurruka masu muhimmanci da kuma tattaunawa kan ababan da aka haɗu akan su.
Za a gudanar da taron ne daga ranar Alhamis, 24, zuwa Litinin, 28 ga watan Satumba, 2024.
