Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamiti da zai binciki cibiyoyin koyar da kiwon lafiya domin gano kwasa-kwasai da ake koyarwa ba tare da izini ba.
Da yake jawabi bayan ya ƙaddamar da kwamitin, mataimakin gwamnan jihar Faruk Lawal Joɓe yace wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan ƙorafe ƙorafe da al’ummar jihar suka yi ne akan tsarin koyarwa na cibiyoyin.
“Saboda ƙorafe ƙorafe da juma’a su kai tayi akan irin kwasa-kwasai da cibiyoyin koyar da kiwon lafiya suka yi gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa wannan kwamiti domin a sami daidaito da buƙatun al’ummar jihar.
Ya ce an bai wa kwamitin wa’adin mako biyu ya miƙa rahoton sa.
Kwamitin na da kwamishinan kasafin kuɗin da tsare tsare Dr Faisal Umar kaita a matsayin shugaba, sauran sun haɗa da Dr Bashir Usman Ruwan Godiya da Rabiu Abba Ruma.
Dr Mu’awiyah Aliyu da babban mai binciken kuɗi na jihar da kuma wakili daga ofishin shugaban ma’aikata na jihar .
Kwamitin zai duba kwasa-kwasai da ake koyarwa don tabbatar da suna da izinin hukuma.
Haka kuma yayi nazari kwasa-kwasan da ake koyarwa a cibiyoyin tare da cire waɗanda ba a sami izinin yin su ba.