Daga JOHN D WADA a Lafiya
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin yi wa ‘yan mata masu shekaru tsakanin shekara 9 zuwa 14 rigakafi domin kare su daga kamuwa da cutar sankarar mahaifa da ta mama.
Dokta Mohammed Addis, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Nasarawa, NPHDA, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi ranar Alhamis a Lafiya.
Ismaila Oko, Manajan Shirye-Shirye, Cibiyar Kula da Rigakafi na Gaggawa ta Jiha ne ya wakilci shugaban a wajen taron.
Dokta Addis ya bayyana cewa jihar Nasarawa na cikin jihohi 16 da aka zaɓa a matakin farko na aikin rigakafin.
Ya bayyana cewa an riga an sayo alluran rigakafin kuma a halin yanzu ana ajiye da su a jihar domin rabawa zuwa cibiyoyi daban-daban.
Don haka ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Gwamna Abdullahi Sule da kuma Dokta Faisal Shu’aib, babban darakta na hukumar kula da lafiya matakin farko na ƙasa, kan rawar da suke takawa wajen ganin an samar da allurar rigakafin a jihohin da aka fara gwajin.
A nasa vangaren, Oko ya ce cutar sankarar mahaifa da ta mama ne ke da kusan kashi 50 cikin 100 na mace-macen da ke da nasaba da kansa.