Deco ya zama sabon daraktan wasannin Barcelona

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon ɗan wasan Barcelona Deco ya zama sabon daraktan wasanni a ƙungiyar

Ɗan ƙasar Portugal haifaffen Brazil, mai shekara 45, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara uku a Nou Camp.

Deco ya fara komawa Barcelona ne daga Porto a shekara ta 2004 kuma ya lashe gasar La Liga sau biyu a kakar wasanni hudu, da kuma gasar Zakarun Turai a shekarar 2006.

Barca ta ce Deco ne zai jagoranci sabuwar aƙidar wasansu kuma zai yi aiki tare da koci Xavi da sauran ma su taimaka masa.

Ƙungiyar ta ce, tana shirin yi wa ɓangaren gudarwarta garambawul, inda ba da cikakkun bayanai nan da makonni masu zuwa.

Tsohon daraktan wasanni Jordi Cruyff ya bar ƙungiyar a watan Mayu.

Deco ya kuma buga kakar wasa biyu a Chelsea bayan zamansa a Sifaniya kafin ya koma Brazil inda ya yi ritaya a ƙungiyar Fluminense da ke Rio de Janeiro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *