Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da cibiyar sauya fasalin mota zuwa CNG a Jihar Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabuwar cibiyar sauya fasalin motoci da ababen hawa daga masu amfani da man fetur zuwa masu amfani da iskar gas na CNG a garin Gundutse dake ƙaramar hukumar Kura a jihar Kano.

Oluwemimo Joseph Osanipin, wanda shine Babban Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar Kula da Kera Motoci ta Ƙasa ne ya bayyana hakan a ranar litinin yayin ƙaddamar da cibiyar, inda ya ce kafa cibiyar zai inganta sauya motoci zuwa masu amfani da CNG tare da ba da horo ga makanikai kan yadda zasu dinga yin sauyin.

Ya kara da cewa, daga cikin cibiyoyi 21 na CNG da aka tsara yi a faɗin ƙasar nan, 15 sun samu cikakkun kayan aiki, inda ake sa ran kammala sauran cibiyoyin nan ba da daɗewa ba.

Osanipin ya buƙaci waɗanda aka horas da su yi amfani da damar da suka samu wajen koyon fasahar sauya fasalin mota zuwa CNG don kaiwa ga cimma burin da ake so na samar da sassauƙan yanayi ga ma’abota sufuri a faɗin ƙasar.

By ukarofi