Ba za mu rasa jin yadda labaru da su ka shafi babbar jam’iyyar adawa PDP a ‘yan kwanakin nan ba. Haƙiƙa duk da rasa mulki da jam’iyyar ta yi fiye da shekaru 9da su ka wuce har yanzu PDP ce mafi girman jam’iyyar adawa musamman ta ɓangaren yawan gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin tarayya. Duk ma babban zaɓe da a ka yi daga 2015 da jam’iyyar ta sha kaye a hannun APC mai mulki a yanzu, ita ke zuwa ta biyu da yawan ƙuri’a. Kazalika baya ga a zaɓen 2015 da tsohon shugaba Jonathan ya gaza nasara inda tsohon shugaba Buhari ya lashe zaɓen amma bai ƙalubalanci sakamakon a kotu ba, sauran zaɓukan da su ka biyo baya na 2019 inda Atiku Abubakar ya yi wa PDP takara da 2023 da ya sake maimaitawa duk PDP da ɗan takarar ta sun kai ƙara kotu har zuwa Kotun ƙoli.
Kalubalantar sakamakon zaɓe na nuna dan takara ko jam’iyya na ɗaukar an tabka maguɗi a zaɓe don haka ba zaɓi sai garzayawa kotu don ƙalubalantar sakamakon. Duk da an samu wasu daga manyan jam’iyyar hatta tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle sun sauya sheka zuwa APC, hakan bai sa an rasa wasu da su ka zauna a jam’iyyar da tunanin wataran za ta iya komawa madafun iko. Mu koma zaɓen 2015 da PDP ta faɗi zaɓe, an samu wasu ‘ya’yanta da su ka haɗa da tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Sokoto Aliyu Magatakarda Wamakko da irin tsohon gwamnan Ribas Rotimi Amaechi sun tattara kayan su sun shiga APC. Haƙiƙa sauya shekar waɗannan na daga dalilan da su ka kawowa PDP tangarɗa har ta sha kaye bayan mulkin tsawon shekaru 16.
Kai hatta shi kan sa ɗan takarar na PDP Atiku Abubakar ya haɗa kai da tafiyar APC ya taya ta kayar da PDP a zaɓen na 2015 duk da daga bisani ya koma cikin lemar sa. Uwa uba ma tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da a ke ganin ya fi kowa cin gajiyar PDP ya ɗau matakin fito bainar jama’a ya keta katin shaidar sa ta zama dan PDP. Matakin ya kara zubar da ƙarfin jam’iyyar har ta kai ga ta samu bakin jinin da har wasu ke lullube kamar makara da alamun PDP don alamta cewa jam’iyyar ta mutu. Kazalika an ɗora alhakin taɓarɓarewar tsaro ta arwa maso gabar wato fitar Boko Haram kan PDP. Ba lalle wasu zarge-zargen gaskiya ba ne amma wasu dalilan zargin murdiya a PDP da cin hanci da rashawa ya ja wa jam’iyyar baƙin jini. Bayan faɗuwa zaɓe tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Sanata Walid Jibrin ya ce za su karɓi aron tsuntsiyar APC su share matsalolin da ke addabar PDP don samun gyaran da zai sake dawo da kurwar jam’iyyar. Ba za ku rasa jin zargin da wasu masu sharhi su ka yi wa tsohon shugaban jam’iyyar Ahmed Mu’azu da barin ƙofa loko-lolo har ta kai ga nasarar tsohon shugaba Buhari na APC a zaben.
Wani abun dubawa ma shi kan sa tsohon shugaba Jonathan ya zama tamkar ɗan jam’iyyar APC don yadda ya kan kai ziyara ga tsohon shugaba Buhari su yi ta dariya kamar ba wata hamaiya da ta taɓa shiga tsakani. Jonathan ma a wani matakin ya mara baya gad an takarar gwamna na APC a zaɓen gwamnan jihar sa ta Bayelsa Mr.Daɓid Lyon. Akasi da a ka samu na kai ƙarar Lyon da takara da mataimaki da ke da matsala ada takardun makaranta ya sa ture nasarar Lyon wanda ya lashe zaɓe. Hukuncin kotu ya sa wanda ya zo na biyu a zaɓen wato Dauye Diri na PDP ya haye karaga da hakan ya faranta zuciyar tsohon gwamnana jihar Serikae Dickson.
Duk mai sanya ido kan sabuwar dimokraɗiyyar Nijeriya daga 1999 zai fahimci da zarar ɗan takara ya samu tikiti a PDP to ba wani mamaki in ya lashe zaɓe. Reshe ya juye da mujiya bayan 2015 inda APC ta dau taurarin zaɓen. Wasa-wasa PDP ta dauka za ta iya dawowa karagar Aso Rock a 2019 amma haka tsohon shugaba Buhari ya zarce. Hukumar zaɓe INEC kan bayyana cewa duk wanda bai gamsu da sakamako bay a garzaya kotu amma ba wanda ya taba ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa ya samu nasara a tarihin siyasar Nijeriya. An kusa samun kawar da shugaba a kotu a zaɓen 2007 inda alƙalan ƙotun ƙoli 3 su ka soke zaɓen marigayi shugaba Umaru ‘Yar’adua da bada hukuncin shirya sabon zaɓe a kwana 90. Rukuni na biyu na wasu alƙalan 3 su ka mara baya ga nasarar zaɓen ’Yar’adua. Marigayi babban alƙali a lokacin Idris Legbo Kutigi ya zama raba gardama inda ya mara baya ga zaɓen shikenan ya kori ƙarar. An kafa kwamitin gyaran tsarin zaɓe ƙarƙashin babban alƙali Lawal Uwais wand aba mamaki ya kawo aƙalla gyaran jiran a kammala tattara sakamako kafin bayyana sakamako sabanon yadda ya faru musamman a 2007 inda tsohon shugaban hukumar zaɓe Farfesa Maurice Iwu ya ayyana sakamakon zaɓen gabanin kammala tattara sakamakon.
Tarihi kan yabawa marigayi shugaba ‘Yar’adua na PDP wanda ya ci gajiyar zaben amma ya fito fili ya ce akwai kura-kurai a gudanar da zaɓen da ya kawo shi kan karaga!. Tsohon shugaban hukumar zaɓe Farfesa Attahiru Jega wanda ya jagoranci zaɓen 2011 ya sha matuƙar caccaka har ma da tsinuwa daga wasu ‘yan gani-kashenin tsohon shugaba Buhari don ayyana tsohon shugaba Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Da Allah ya ba wa Farfesa Jega damar jagorantar zaɓen 2015 kuma ya ayyana tsohon shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaɓe sai ‘yan gani-kashenin su ka juya sukar zuwa yabo duk da ‘yan gani-kashenin PDP irin tsohon minista Godsday Orubebe sun caccaki Jega da cewa ya yi ha’inci. Haka siyasar Nijeriya ke gudana inda yawanci in an samu nasara to ga wanda ya samu an yi gaskiya in an rasa kuma a ambaci akasin hakan. Duk da haka ‘yan siyasa na tutiyar cewa mafi lalacewar jagoarancin su ya fi mafi ingancin mulkin soja a’ala ga ƙasa.
Babbar jam’iyyar adawar Nijeriya PDP ta faɗa rikicin shugabanci tsakanin magoya bayan gwamnonin jam’iyyar da kuma ɓangaren ministan Abuja Nyesom Wike.
An tabbatar masu biyayya ga ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar ƙarƙashin gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad na son tabbatar da ’yancin jam’iyyar daga duk wani kutse a waje da jam’iyyar.
Alamu na nuna muƙaddashin shugaban jam’iyyar Umar Iliya Damagun na bin hanyoyin kai labari bayan ɗaya daga ‘yan kwamitin zartarwa najam’iyyar Ahmed Yayari ya fitar da sanarwar amsar ragamar jam’iyyar.
Tun bayan zaɓen 2023 a ke samun baraka a jam’iyyar da gaza dakatar da tsohon gwamnan Ribas Nyesom Wike wanda a fili ya yaƙi jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa.
Za a jira a ga yadda jam’iyyar za ta iya sulhunta wannan babbar baraka da ta fuskanta da ke cikin mafiya damuwa tun rasa madafun iko a 2015
Mun magance barakar mu ta PDP – Gwamna Bala:
Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammed ya bayyana cewa sun magance barakar da ke cikin jam’iyyar su ta PDP.
In a na bin labaru dai PDP ta nemi ɓangarewa gida biyu inda muƙaddashin shugaban jam’iyyar Umar Damagun ya dakatar da sakataren labaru Debo Olugunagba da jami’in shari’a Kameleddin daga jam’iyyar.
Ba bata lokaci ɓangaren jam’iyyar ta sanarwar Olugunagba sai ya dakatar da muƙaddashin shugaban jam’iyyar Damagun da sakatare Anyanwu inda kuma ya aiyana Ahmed Yayari a matsayin shugaban jam’iyyar.
Gwamna Bala Muhammed a matsayin shugaban majalisar gwamnonin jam’iyyar ya nuna tamkar ba a ma samu baraka a jam’iyyar ba don an sasanta kuma duk wanda a ka dakatar an dawo da shi.
Gwamna Muhammed na magana ne bayan taron gwamnonin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki na kwamitin gudanarwa inda ya ce yanzu kowa ya koma kan mukamin san a asali har zuwa taron majalisar ƙolin jam’iyyar da a ke shirya za a gudanar ranar 25 ga watan nan.
A na hasashen za a ba wa Damagun dama a mutunce ya sauka daga mukamin inda za a miƙa ragama ga yankin arewa ta tsakiya ya fito da wanda zai jagoranci jam’iyyar, wato ya ɗau kujerar shugaban jam’iyyar na asali Iyorchia Ayu da ƙarar da a ka shigar da shi kotu bayan dakatar da shi daga jam’iyya da mazaɓar sa a Binuwai ta yi, ya sa shi zakuɗawa gefe.
Bincike ya nuna wasu gwamnonin PDP na mara baya ga tsohon gwamnan Ribas wato ministan Abuja Nyesom Wike wanda kuma a ke zargin muƙaddashin shugaban jam’iyyar Damagun ke tare da tafiyar.
Kazalika yunƙurin wasu gwamnoni da ma ‘yan majalisar dokokin taraiya na PDP ya jawo ayyana ma’ajin jam’iyyarAhmed Yayari a matsayin muƙaddashin shugaba don karya lagon Wike da su ke ganin ya zama kadangaren bakin tulu a jam’iyyar.
Kammalawa;
Shin PDP za ta iya dakatar da Nyesom Wike ko kuwa a’a, duk wanda Allah ya raya zuwa babban zaɓen 2027 zai ga wasu sabbin lamura ko da kuwa APC ba ta fadi zaɓe ba. PDP ta yi shekaru 16 kafin rasa madafu inda a ke duba ko shekaru nawa APC za ta samu? Shin dimokraɗiyya ta yi wa talakawa amfani ko akasin hakan an ga taka rawar kowane irin dan siyasa na ɓangaren hagu ko dama.
