Za a yi zaɓen ƙananan hukumomin Kano duk da hukuncin kotu – Ɗan Majalisa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A kwanaki biyu da suka gabata ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin dakatar da Hukumar zaɓe ta jihar (KANSIEC) daga gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.

Kotun ta yi hakan ne bayan wani zargi da ta yi da ke alaƙanta jagororin hukumar da wata jami’yya a jihar wanda hakan ya saɓa wa dokar hukumar a mataki na jiha da ma ƙasa baki ɗaya.

Duk da wannan hukunci da kotun ta yi, shirye-shirye game da zaɓen na cigaba da gudana yadda aka tsara, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Daga cikin ayyukan zaɓen akwai ɗaukar ma’aikatan da za su yi aikin zaɓen da kuma jami’an ƴan sanda da na ‘Civil Defence’ da ke ofishin hukumar suna kula kai-kowa da ke gudana a ƙarƙashin shirye-shiryen.

Shugaban mafi rinjaye na Majalisar Dokokin jihar, Lawal Hussaini Chediyar Ƴar Gurasa ya bada tabbacin za a gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara shi, ya na mai cewa suna da umarni daga kotun na haramtawa jam’iyyu 19 dakatar da zaɓen.

Ya kuma ce za gudanar da zaɓukan ba tare da ƴan sanda suna wuraren ba inda ya ce ƴan ƙasa masu kishi zasu tsare akwatinan zaɓen.

Saidai, al’umma da ƙwararru a harakar siyaysa da shari’a na kallon hakan a matsayin bijire wa umarnin kotu wanda ka iya haifar da ƙalubale a nan gaba.

By Babaji