Sarki Sanusi zai naɗa Ali Muktar a matsayin sabon Sa’in Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a 25 ga watan Oktoba, 2024 ne Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai naɗa sabon Sa’in Kano.

Za a gudanar da taron naɗin ne a Masallacin gidan Sarki da ke Kofar Kudu a Kano, da misalin ƙarfe 9 na safe.

Arc. Ali Muktar, shi ne wanda za a bai wa Sarautar Sa’in kuma Hakimin Makoɗa.

Cikin wata takarda da Matawallen Kano, Aliyu Ibrahim Ahmed ya aika masa, ya taya shi murna game samun matsayin, ya na mai kira a gare shi da ya sanar da ƴanuwa da abokan arziƙi don su taya shi murna gami da yi masa fatan alheri.

By Babaji