Fadar shugaban ƙasa ta sanar da sabon naɗe-naɗen ministoci tare da sake fasalin ma’aikatu, wanda zai taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati da gudanar da harkokin mulki a ƙasar. Wannan sanarwar ta zo ne a watan Oktoba 2024, inda aka bayyana wasu canje-canje masu muhimmanci da suka shafi naɗe-naɗen ministoci, sauya ma’aikatu, da kuma sallamar wasu ministoci daga majalisar zartarwa.
Daga cikin manyan sauye-sauyen da aka yi, akwai haɗa ma’aikatar yawon buɗe ido da ma’aikatar al’adu ta tarayya don zama ma’aikatar al’adu, yawon buɗe Ido, da tattalin arziki na Ƙirƙire-ƙirƙire. Wannan matakin an ɗauke shi ne domin ƙara haɗa kai da ɓunƙasa tattalin arziki ta hanyar Ƙirƙire-ƙirƙire da al’adu. Haka kuma, an sake tura ministoci goma zuwa sabbin ma’aikatu, yayin da aka sallami wasu ministoci guda biyar daga ayyukansu.
Daga cikin ministocin da aka sauyawa ma’aikatu, akwai Hon. Dr. Yusuf Tanko Sununu, wanda ya koma ma’aikatar jinƙai da rage talauci, sai Dr. Morufu Olatunji Alausa da ya zama ministan ilimi.
Haka zalika, Barr. Bello Muhammad Goronyo an mayar da shi ƙaramin ministan ayyuka, yayin da Hon. Abubakar Eshiokpekha Momoh ya koma matsayin ministan ci gaban yankunan ƙasa. An kuma naɗa Dr. Doris Uzoka-Anite a matsayin ƙaramar ministan Kuɗi, sai kuma Imaan Sulaiman-Ibrahim, wacce yanzu ta zama ministan harkokin mata.
A mataki na sauye-sauye, wasu ministoci guda biyar sun rasa kujerunsu, wanda suka haɗa da Barr. Uju-Ken Ohanenye, tsohuwar ministan harkokin mata da Lola Ade-John, tsohuwar ministan yawon buɗe ido.
Haka nan, Prof. Tahir Mamman wanda ya riƙe kujerar ministan ilimi shi ma yana daga cikin ministocin da aka sallama daga bakin aiki.
A hannu guda, akwai nadin sabbin ministoci bakwai, ciki har da Dr. Nentawe Yilwatda, wanda aka naɗa a matsayin Ministan jinƙai da rage talauci, da Muhammadu Maigari Dingyadi da aka naɗa ministan Ƙwadago da ayyuka. Haka kuma, an naɗa wasu ministoci kamar Bianca Odumegwu-Ojukwu da Dr. Jumoke Oduwole a sabbin kujeru da aka ƙirƙira.
A karshe, Shugaban ƙasa ya gode wa ministocin da suka yi aiki tare da shi, musamman waɗanda aka sallama, bisa ga irin gudummawar da suka bayar ga ci gaban ƙasa. Ya kuma yi kira ga sabbin ministoci da waɗanda aka sake tura su ga sabbin ma’aikatu, su ɗauki wannan matsayin a matsayin kiran bauta wa ƙasa tare da nuna jajircewa domin tabbatar da ci gaban Nijeriya bisa tsare-tsare da ƙudurorin gwamnati.
