Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin ‘N-Knowledge’ don horas da matasa

Daga WAKILINMU

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa gwamnati ta soma wani sabon shiri mai suna ‘N-Knowledge’ domin tallafa wa matasan Nijeriya su koyi aikin yi a ɓangaren fasahar zamani.

A wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Bashir Nura Alƙali, ya bayyana cewa an fara shirin ne a dukkan sassa shida na ƙasar nan tare da Yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja, kuma wani ɓangare ne na shirin nan na ‘N-Power’.

Alƙali ya ce, “‘N-Knowledge’ wani ɓangare ne na shirin ‘N-Power’ wanda zai maida hankali ga bai wa matasan Nijeriya horaswar da ta kamata tare da satifiket domin su zama ƙwararrun ma’aikata, masu ƙirƙira kuma ‘yan kasuwa da za su iya yin aiki a cikin gida da ƙasar waje.

“Shirin na ‘N-Power (N-Knowledge)’ zai horas da matasa 20,000 daidai da muradin duniya a matsayin waɗanda za su iya yin aiki a ƙasashen waje a ɓangaren fasahar harkokin komfuta da intanet.”

Babban Sakataren ya ce an tsara ɓangaren horaswa na shirin ne don bunƙasa ƙwarewar matasan wajen ƙirƙirar manhaja da horaswa kan haɗawa da gyara kayan aikin komfuta wanda zai sanya Nijeriya ta shiga sahun ƙasashen da ke tura ma’aikata zuwa wasu ƙasashen domin su yi aikin haɗa manhaja.

A cewar sa, “Shirin zai samar da ƙwarewa da iyawa a fagen tsara manhajojin wayar hannu da gina gidajen yana tare da inganta basira don a haɓaka masana’antar fasahar yaɗa labarai da ilimin intanet a Nijeriya.

“Shirin ya ƙunshi aje matasa a wani keɓaɓɓen wuri ana horas da su har tsawon wata uku sannan a ba su aikin wucin gadi na wata shida a dukkan sassa shida na ƙasar nan.

“Jimillar mutum 20,000 za su ci moriyar shirin.”

Ya ƙara da cewa a ƙarshen shirin, matasan da aka gamsu da cancantar su daga horaswar da aka yi masu za a ba su satifiket da takardun shaida.

Ya ce, “A lokacin wannan tirenin ɗin za a yi masu karatu daban-daban wanda ba shakka zai ƙara masu sanin makamar aiki har su kasance sun shirya wa shiga duk wata gogayya a duniya wajen aiki.

“Wannan ya na da muhimmanci domin kuwa waɗanda aka horas ɗin za a koya masu darussan da za su amfane su a iya tsawon rayuwar su tare da sauya masu tunani, da ɗabi’u nagari na gudanar da aiki a yayin da kuma ake karantar da su ƙa’idojin yin mu’amala da juna.”