Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin biyan Masu Yi Wa ƙasa Hidima (NYSC) cikon alawus mafi ƙaranci na watannin baya da ba a biya su ba.
Ministan Cigaban Matasa Ayodele Olawande ya tabbatar da shirin biyan kuɗin a ranar Litinin yayin da yake hira da gidan Talabijin na Channels a shirin Siyasa A Yau.
Olawande ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗaɗen alawus N77,000 da suka haɗa da kuɗaɗen da aka dawo da su, ga duka mambobin NYSC da kuma waɗanda ke shirin shiga.
Bayanin nasa ya biyo bayan kalaman darakta Janar na NYSC, Olakunle Nafiu, wanda ya tabbatar wa mambobin a makon da ya gabata cewa za a fara aiwatar da sabon alawus ɗin ne a watan Maris na 2025.
Tun a watan Satumban 2024 ne gwamnatin ƙasar ta amince da biyan su sabon alawus mafi ƙaranci na naira 77,000 daga naira 33,000 da ake biyan su, sai dai kawo yanzu ba su kai ga cin gajiyar ƙarin ba.
Haka kuma a watan Maris da muke ciki ne ake sa ran masu yi wa aasa hidimar za su fara karɓan sabon alawus ɗin.
Hakan dai na zuwa ne yayin da miliyoyin ’yan ƙasar ke fama da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki saboda janye tallafin man fetur da wasu manufofin da gwamnati ta fito da su.
Lamarin da ya sa wasu masu sharhi ke ganin ƙarin alawus ɗin bai taka kara ya karya ba.
