Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Tun mu na Islamiyya za ka ji a na cewa ai ranar lahira al’umma za su kama yawace-yawace tsakanin annabawa, tun daga kan Nuhu su na neman ceto, su Ibrahima, Musa da Isa kowa ya ce ta kai ne yake. Sai an zo wajen manzon Allah sai ya amshi jama’a ya ja zuga gaban Allah ya na cewa “Ummati… ummati”.
Cikakken bayanin ya zo cikin hadisin Bukhari na 4712 a sashen tafseer, ya na da tsawo hadisin. Wannan hadisi ya yi karo kai tsaye da ayoyin ƙurani.
Na farko shi ne ayoyin cikin Suratul Furƙan, da Allah ya yi ma na bayanin abinda zai wakana a wannan rana Q25:26 “Mulki a rãnar nan, na gaskiya, yanã ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kãfirai, mai tsanani” A wannan rana duk wanda ya kauce wa Allah da manzanni, babu komai tare da shi da zai iya fansar kansa, saboda dama ta je masa amma bai yi amfani da ita ba.
Mutum zai zargi kansa da kansa Q25:27 “Kuma rãnar da azzãlumi yake cĩzo a kan hannayensa, yanã cẽwa ”Ya kaitõna! (A ce dai) na riƙi hanya tãre da Manzo!”
Wace ce hanyar Manzo?
Q28-29 “‘Ya kaitõna! (a ce dai) ban riƙi wãne masõyi ba!’ ‘Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga ambato (ƙurani) a bãyan ya je mini.”Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum.”
Wanen ka kuwa shine duk wani abu da ya sa ka rabu da ƙurani, ka rike shi a maimakonsa. Wato duk abinda ka bi wanda ya yi karo da umarnin Allah a ƙurani, zai zamo maka shaidan dinka: akidar ka ce, kungiya ce, shehi ne, kimiyya ce, ko jahilci?
Don haka maimaikon cewa annabi zai ruga wajen Allah ya na “ummati…ummati” ga abinda Allah ya tabbatar mana annabin zai yi a wannan rana Q25:30 “Kuma Manzo ya ce: ”Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur’ãni abin ƙauracẽwa!”
Wato akasari sai a ke fassara ayar da cewa kafirai ake nufi a nan. Ko kadan, domin kafirai basu taba karbar kur’ani ba, ballantana su kaurace masa. Allah ya yi amfani da kalmar “Mahjura” wato wanda ke Makka kadai ake kira da Muhajjirun, shine yayi hijira zuwa Madina.
Don haka Annabi karar mu musulmi zai kai wajen Allah cewa bayan ya ida sakonsa daga baya mutane sun kauracewa ƙurani sun maye gurbinsu da kirkirarrun hadisai da fatawoyin malamai da su ka ci karo da ƙur’ani.
Ta kai cewa yanzu duk inda ake son karkata musulmi sai a kawo hadisi ko wata fahimta ta akida amma babu la’akari da me ƙurani ya ce. Akwai ma wadanda ke cewa Hadisin na iya shafe ƙurani.
Abu na biyu da wancan hadisi ya ci karo da ƙurani shine a karshen hadisi wai sai ya ce “Na rantse da wanda rai na ke hannunsa, nisa tsakanin wannan kofa ta aljanna da makwabciyarta daidai ya ke da nisa tsakanin garin Makka da birnin Basrah” Wato nisan da bai wuce kilomita 1500 fa kenan.
Bayan Allah ya yi mana bayanin girman aljanna a ƙurani da cewa Q57:21 “Ku yi tsẽre zuwa ga (nẽman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna (wadda) fãɗinta kamar fãɗin samã da ƙasã ne..”
Ya ilahi, a yanzu haka, fadin sammaiz wato iya wanda muke iya gani kawai banda wanda ba zamu taba iya hange ba har abada, ya kai tafiyar haske ta shekaru biliyan 93.
Wannan adadi wallahi kwakwalwa ba za ta iya hakaito shi ba. Domin haske ya fi komai sauri shi yasa ake ma’auni da shi a tafiya a sammai. Misali Rana tana da nisan kilomita miliyan 150 daga duniya amma cikin minti 8 haskenta ke ratsa wannan nisa yake isowa duniya.
Tafiyar haske a shekara kuwa kilomita Tiriliyan 9.5…idan zaka ratsa wannan sammai ta mu sai kayi tafiyar wannan adadi sau shekaru biliyan 93…subhanaka ahsanul khaliƙin. Wallahi kwakwalwarmu ba ta da mazaunin da zai iya daukar wannan lissafi.
Don haka jama’ar musulmi mu gane cewa bamu da wani kalubale a wannan zamani irin yadda shaidan ya raba mu da ƙurani, kuma hakan ne zai zama korafin Annabi na farko a ranar lahira a kan mu. Gidan kowa akwai ƙurani amma sai dai mu yi masa karatun aku, saboda akasarinmu ba mu iya larabcin da zamu fahimta ba. Wadanda su ka iya Larabcin ma a wake suke bita ba tare da tafakkurin ma’anoninsa ba.
Shi ya sa Allah har gori ya ke mana da cewa Q54:17 “Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur’ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? Wanda Allah ya baiwa ikon karantawa da aiki da shi, zai tsira daga tuhumar da manzo zai yi mana a gaban ubangiji Q25:30 “Kuma Manzo ya ce: ”Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur’ãni abin ƙauracẽwa!”
A karshe, wajibi mu gane cewa dole mu dauki Alƙur’ani a matsayin matankadi na hadisai da duk wani ilimi saboda mun yi imani cewa ba shi da wani kuskure a tattare da shi. To don me muka yarda a ke raba mu da shi? Ga shi a hannunmu amma ba ma aiki da shi.
