Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Da ni da kai da sauran dabbobi duk mu na da kwakwalwa, amma abinda ya banbanta mu da dabbobi shine kwakwalwarmu na da hankali, wannan hankali idan muka yi amfani da tunani sai ya banbance mana aya da tsakuwa, fari da baki, mai kyau da mara kyau.
Shi yasa Allah ya ce mana cikin Q38:29 “(Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni.”
Wato duk wani Dan Adam (idan banda maras lafiya – wato mahaukaci, ko yaron da bai mallaki hankalinsa ba) ya na da hankali, amma wannan hankalin ba shi da amfani matukar bai yarda zai yi tunani da wannan hankalin da Allah ya ba shi ba.
Idan Dan Adam ya gaza yin amfani da tunani, duk da hankalin nan da Allah ya ba shi, sai ya yi zamiya ya zama Dabba ma ta fi shi. Q25:44 “Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã tunani da hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida suke. Ã’a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.”
To, wannan yanayi shine annobar da ta fada mana a yau, wato sai mu ka kasance a yau gara dabbobi da mu, domin ga hankalin, amma mun yi watsi da tunani, walau a mu’amala, zamantakewa, siyasa kai har ma a harkokin addininmu.
Cikin jerin ayoyin da suka biyo bayan wannan gargadi na cewa kada mu zama dabbobi sai Allah ya jero irin tunanin da yake son mu yi, cewa Q25:45-47 “Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã Yã bar ta tsaye cif, sa’an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta. Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã yini ya zama lokacin tãshi (kamar Tashin kiyãma). Kuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamarSa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama.”
Dabbobi kaf, ba ruwansu da duk wadannan, mutane masu tunani da hankalinsu kadai su ne zasu gane hikimomi na kimiyyar rayuwa, yadda Rana da wata da dare da yini ke nuna mana mahaliccinsu. Wato Ilimi na zahiri da kwakwalwa ke iya tsinkayarsu.
Sannan a can gaba Kuma sai ya ce, ƙ25:50 “Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa shi (Alƙur’ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci.”
To, hatta ƙurani da Allah ya shimfida mana shari’o’i cikinsa bai saukar da shi kawai a karanta ba, sai dai domin a yi tafakkurin ayoyinsa. Wannan tsari na tunani game da ayoyin Allah shine ke banbanta mutane zuwa azuzuwa biyu, wato masu karatu da masu Ilimi. Banbancin karatu shine kowa zai iya zama mai karatu idan ya bi tsarin da muke da shi na hadda da kira’a da fassara, amma sai ainihin wadanda ke tunani a game da ayoyin kadai ke iya riskuwa ga ilimin da ke ciki. A yanzu akasari sai ka ga cewa hatta masu kiran kansu malamai, iya karatun kawai su ka tsaya babu ilimin, saboda sun ginawa kansu ka’idar kawai su bi wata fahimta wadda ta jingina da wata akida ta su kawai. Babu fadada tunani da bin tsarin ainihin zakulo ma’ana da ayoyin ke nufi. Ballanta mabiya wadanda da ma ba aikinsu ba ne.
Cikakken misali na hurumin tunani sama da komai, hatta a kan Imani shine labarin Ibrahima a suratul Baƙara da ya nemi Allah ya nuna masa yadda ya ke fitar da Mai Rai daga matacce. Har Allah ya ce masa, ƙ2:260 “Ya ce “Shin Kuma baka yi Imani ba ne?” Ya ce “Na’am” Kuma amma domin zuciyata ta nutsu.”
Wato a nan Ibrahim na son ya nuna mana cewa Imani kansa na samun gamsuwa ne daga “Ilmul Yaƙin” wato Ilimi na yankan shakku wanda ba ya samuwa sai ta hanyar nazari da bincike. Abinda Malaman zamani ke yaki dashi, tare da assasa hanyar Imani Ido rufe da magabata.
Wannan ya sa mun dauki hanyar da ta karkatar da Yahudu da Kiristoci wadda Allah ya gargade mu cikin Q62:5 “Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa’an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai.”
Da kuma wanda yayi gargadi a cikin Q9:31 “Sun riƙi mãlamansu (Yahũdu) da ruhubãnãwansu (Nasãra) Ubannangiji, baicin Allah.”
Wato duk wadannan gargadin guda biyu, babu wanda bai cimmana ba kamar yadda Allah ya sa ke gargadin mu cewa tamkar yadda Yahudu da Nasara su ka fada wannan komar, to mu ma mun fada sai wanda Allah ya tsare Q25:31 “Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga mãsu laifi ga kõwane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako.”
Wato mutanen Manzon Allah su ma sun fada tarkon wadannan makiya, domin na farko dai ga Ilimi fal cikin ƙurani, amma akasarin musulmi saboda ko dai ba a iya larabcin da za a fahimta ba, ko kuma an barwa wasu kalilan cewa su kadai ke iya fahimtar sa sannan su sanar da mutane. Ka ga akasarin mu, mun zamto tamkar “Jakin da kayan littafai” irin na Yahudu, wato muna dakon Ilimi a kwakwalwarmu, saboda kowa ya iya karanta Qurani, ga shi a rataye cikin gidajenmu, yara kanana kullum na haddarsa, amma rashin sanin me ke kunshe a cikin abinda muke karantawa, tare da rashin aiki da shi sau-da-kafa, ina banbancin mu da jakin da ya dauko kayan littafai?
Sannan a daya bangaren, kamar Nasara, kasancewar mun rarrabu kungiya-kungiya, kowacce na ganin cewa ita kadai ce a kan daidai, sauran duk tamkar kafirai su ke, don haka idan ka ce wancan ya na bautar waliyyai da shaihunnai, to shi kuma wancan na bautar Ahlul bayti ne, ko kuwa wancan kuma na bautar sahabbai, ko bautar hadisai. Kowa ya yi riko da abinda ya yi Imani da shi, amma kuma a wawance, duk mun taru mun yi watsi da abu guda, wanda shi kadai ne ya hada mu waje guda, wato shi kansa ƙurani. Ko ba komai kasancewar mu a rarrabe muna yaki ne da umarnin Q3:193 “Kuma ku yi riko da hanyar Allah, kada ku rarraba.”
Saboda tsananin illar rarraba tsakanin musulmi sai Allah ya ja kunnen Manzo da cewa, Q6:59 “Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al’amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa’an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.”
Abu guda da zai hade kanmu shine ƙurani, saboda duk akidarka: ka yarda da sahihancinsa, ka yarda da hukuncinsa, ka yarda babu kuskure a cikinsa, amma kuma ka yarda a nesanta ka da shi? Ko a fifita wani abu a kansa?
Wannan dalili ya sa Allah ya jefe mu da kalubale cewa a ranar lahira, Manzon Allah kararmu zai kai gaban Allah cewa, Q25:30 “Kuma Manzo ya ce: “Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur’ãni abin ƙauracẽwa!”
Wallahi duk wandanda su ka sake shaidanu na mutane da aljanu su ka ci gaba da raba su da ƙurani, ko fifita wani tsari na shiriya fiye da shi, to su sani cewa Allah ya gaya mana irin da-na-sanin da za su fuskanta a cikin Q25:29 “Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunãwa (wato ƙurani) a bãyan (Tunãwar) ta je mini. Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum.”
Wanda zai iya kaucewa wannan hadarin shine wanda ya kasance: Q2;121 “Waɗanda Muka bai wa Littãfi suna karãtunsa a kan haƙƙin karãtunsa, waɗannan suna ĩmani da shi (Alƙur’ãni).
Mene ne hakkin karatunsa? ƙira’a cikin tajwidi da maƙe murya, ko kwaikwayon Larabawa? Ko yi ma sa karatun Aku? Ko kadan ga abinda Allah ke nufi Q38:29 “(Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni.”
A ƙarshe mu sani cewa mafificiyar asara da Mutum zai yi ita ce: Ga kwakwalwa Mai hankali amma wadda ba ta tunani… gara dabba da ita. Ko Musulmi da ya raba kansa da ƙur’ani yà rungumi waninsa a matsayin shiriya.
