Daga AISHA ASAS
A yammacin ranar Talata ne fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdu Kano ko Abdullahi Shu’aibu, wanda aka fi sani da Baba Karƙuzu, ya kwanta dama, inda za mu iya cewa mutuwar tasa ta taɓa mutane da dama, ciki kuwa har da Gwamnatin jiharsa ta Filato, inda jim kaɗan bayan sallar jana’izarsa da aka gudanar da sanyin safiyar ranar Laraba a gidansa da ke Haruna Hadeja Street a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, gwamnatin jihar ta fitar da sanarwar jajentawa tare da miƙa ta’aziyyar rasuwar fitaccen Jarumi Baba Karƙuzu ga iyalansa da kuma abokan sana’arsa.
A cikin ta’aziyyar mai ɗauke da sa hannun, Daraktan Yaɗa Labarai, Gyang Bere, a ranar Laraba, Gwamna Mutfwang ya ce, “Marigayi Karƙuzu ya rayu a matsayin tauraro mai haska rayuwar al’umma har ƙarshen rayuwarsa, inda hakan ke nuni da cewa, rasuwarsa babban rashi ne ga iyalinsa, masana’antar shirya finafinai da Jihar Filato da ma ƙasa bakiɗaya.”
Mutfwang ya kuma jaddada irin gudunmawar da Abdu Kano ya bayar a masana’antar shirya finafinai ta Hausa, inda ya bar bayansa da tambari mai haske ta hanyar ilimintarwa, nishaɗantarwa da wayar da kan al’umma.
Baya ga wannan, ita ma uwar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Kannywood (MOPPAN) ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan fitaccen jarumi, Abdu Kano, wanda aka fi sani da Baba Karƙuzu, bayan rasuwarsa a ranar Talata, 25 ga Maris, 2025.
A wata sanarwa da shugaban MOPPAN, Malam Maikudi Umar (Cashman) ya fitar, ya bayyana rasuwar Karƙuzu a matsayin babban rashi ga masana’antar Kannywood da ɗaukacin al’ummar Arewacin Nijeriya.
Sanarwar ta ce, “Rasuwar wannan babban jarumi, uba, kuma ɗaya daga cikin ginshiƙan da suka aza harsashin wannan masana’anta, babbar rashi ne. Muna addu’a Allah ya gafarta masa, ya sanya shi cikin rahamarsa, sannan ya bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.”
Shugaban ya jaddada cewa Baba ƙarƙuzu ya taka rawar gani wajen ci gaban Kannywood, kuma girmamawa gare shi ba za ta gushe ba a zukatan masoya da abokan aikinsa.
Haka zalika ƙungiyar haɗakar ƙungiyoyi fim ta KAFIGAN ta yi alhini tare da jajenta rasuwar tsohon ɗan wasan fim ɗin Hausa.
Karƙuzu ɗaya ne daga cikin taurarin finafinan Hausa da suka jima suna nishaɗantar da al’umma musamman a ƙasar Hausa, wanda mutuwarsa ta haifar da babban giɓi ga masana’antar, inda zai yi wahala a maye gurbin da ya bari.
Darakta-Janar na KAFIGAN, Hon. Adamu Bello, ya bayyana jimaminsa game da babban rashin tare da masa addu’ar fatan samun rahamar Allah (SWT).
Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalansa da masana’antar Kannywood da ƴaƴanta gami da ɗaukacin al’ummar Hausa.
Haka ma ƙungiyar dattawan Kannywood (Kannywood Foundation) ta nuna alhinin rasuwar ɗaya daga cikin tushen kafuwar masana’antar.
“A madadin ɗaukacin membobin kungiyar dattawan Kannywood, mahukuntan Kannywood Foundation, zuciya cike da alhini muke miƙa ta’aziyyar rasuwar Malam Abdullahi Shuaibu, wanda aka fi sani da Abdu Kano ko kuma Baba Karkuzu a masana’antar finfinan Hausa, wato Kannywood.
“Gudunmawar Karkuzu a masana’antar fim ta Hausa ba zai iya aunuwa ba.”
Ya fara haskawa a matsayin ɗan wasan kwaikwayo a gidan talabijin na Jihar Filato (PRTɓ Jos) a da taken Karƙuzu na Bodara inda ya samu fitaccen sunan nasa da har yau aka kiranshi da shi.
Irin rawar da ya taka a sauran finafinan da suka biyo baya sun taimaka wajen tabbatar da matsayinsa na fitaccen jarumi da kuma shahara a masana’antar da ma ƙasa bakiɗaya.
Ya kasance mutum mai sauƙin kai, ban dariya da sauƙin hali. Hakan ya sanya shi a layin waɗanda giɓin da suka bari ke wuyar cikewa.
“ƙungiyar Dattawan Kannywood na alhinin rasuwar wannan fitaccen jarumin barkwanci tare da mika saƙon ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwa da abokan arziki. Muna kuma roƙon Allah ya jikansa da rahama.
Allah Ya jiƙan sa Ya kuma gafarta masa tare da bai wa ƴan uwa da abokan arziƙi haƙurin juriyan rashinsa,” inji sanarwar kai ɗauke sa hannun kakakin Kannywood Foundation, Malam Kabiru Maikaba.
