Eidl-el Fitr: Gwamnan Zamfara ya yi kira kan haɗin kai, zaman lafiya da cigaban jihar

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya roƙi al’ummar jihar da su rungumi haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban jihar.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wani jawabin barka da Sallah ga alummar jihar a lokacin da yake taya al’ummar Musulmi murnar kawo ƙarshen watan azumin Ramadan a yau ranar Lahadi.

Ya buƙaci al’ummar Musulmin Jihar Zamfara da sauran ƙasashen duniya da su zurfafa tunani kan sadaukarwa da sadaukar da kai ga Allah da aka yi a cikin watan Ramadan.

“Ya ku ‘yan uwana musulmi na Jihar Zamfara da sauran ƙasashen duniya, ina miƙa saƙon barka da sallah da kuma taya murna da kammala azumin watan Ramadan na shekara ta 1446 bayan hijira”.

Ya ce watan Ramadan ya kasance lokaci ne na zurfafa tunani, sadaukarwa, da ibada ga Allah SWT.

“Yayin da muke gudanar da bukukuwan ƙaramar Sallah, ina kira ga kowannenmu da ya ci gaba da ayyukan ɗa’a, da haƙuri, da karamcin da Ramadan ya cusa mana.

“ƙalubalan da ke gabanmu suna da yawa kuma suna buƙatar haɗin kai don ganin an magance su, don haka mu ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu yi aiki tare a matsayin al’umma ɗaya, mu goyi bayan ajandar gwamnati na ceto da sake gina jiharmu. Yace

Gwamna Lawal ya kuma yaba da ƙoƙarin shugabannin addini da na al’umma bisa yadda suke ci gaba da jajircewa wajen ciyar da zaman lafiya da inganta ɗabi’un da ke haɗe mutane wuri guda.

“Yayin da muke taruwa da masoyanmu domin murnar wannan gagarumin biki, bari mu sanya jiharmu cikin addu’o’in neman taimakon Allah yayin da muke aiki ba dare ba rana domin magance ɗimbin ƙalubalen da jiharmu ke fuskanta.”

By ukarofi