Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wani matashi bisa zargin kashe ɗan bijilante

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Usman Sagiru, ɗan shekara 20 daga unguwar Sharifai, bisa zargin hannu a kisan da kuma harin da aka kai wa wasu ‘yan bijilante a lokacin dawowar sarki Muhammadu Sanusi II daga sallar idi a ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025, da misalin ƙarfe 12:40 na rana.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, Usman Sagiru tare da wasu da har yanzu ba a kama ba, sun daɓa wa Surajo Rabiu, ɗan bijilante daga Sabon Titi Jaba Quarters wuƙa, wanda daga baya ya mutu sakamakon raunin da ya samu. Haka kuma wani ɗan bijilante, Aminu Suleman daga unguwar Ƙofar Mata, ya ji raunuka kuma yana karbar magani a asibitin ƙwararru na Murtala Mohammed, Kano.

Rundunar ta ce ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da gayyatar Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin yi masa tambayoyi.

Haka kuma, rundunar ‘yan sandan ta jaddada haramcin gudanar da duk wani biki ko gangamin hawan sallah a Kano, tana mai gargaɗin cewa duk wanda aka kama yana gudanar da irin wannan taro ko wata ɗabia ta daba da ka iya haddasa tashin hankali, za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Daga ƙarshe, rundunar ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

By ukarofi