Shettima ya jagoranci ministoci a ziyarar sallah ga Tinubu

Spread the love

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a yau ya jagoranci tawagar ministoci da sauran jami’an gwamnati domin kai gaisuwar Sallah ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadar shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ziyarar ta biyo bayan sallar idi da aka gudanar da safiyar Lahadi a filin Idi na ƙasa da ke kan titin filin jirgin sama a Abuja, wanda ke nuni da ƙarshen watan Ramadan mai alfarma.

By ukarofi