Ana ci gaba da allawadai da kisan mafarauta a Edo

Spread the love

Ana ci gaba da sukar kisan da aka yi wa fararen hula 16 a Uromi, Jihar Edo, wanda ya faru a ranar Alhamis da ta gabata. Ƙungiyoyi daga Arewa, gwamnatocin jihohi, da ‘yan majalisa sun bayyana matuƙar damuwarsu kan lamarin, suna mai kira da a ɗauki matakin gaggawa.

Rahotanni sun nuna cewa waɗanda aka kashe na kan hanyarsu ta komawa gida daga Jihar Ribas domin yin bukukuwan ƙarshen azumin Ramadan da Sallah tare da iyalansu, kafin su faɗa hannun wasu da suka kai musu hari.

Ƙungiyar dattawan Arewa (NEF) ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin adalci, tana mai buƙatar a bi diddigin waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki. Ita ma Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah wadai da harin, tana mai kira ga hukumomi su tabbatar da adalci ga iyalan mamatan.

Gwamnatin Jihar Kano ta bakin kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Waiya, ta yi kakkausar suka ga lamarin, tana mai buƙatar hukunta duk wanda ke da hannu a kisan. Hakazalika, jam’iyyar PDP reshen Edo ta nuna rashin jin daɗin ta, tana mai zargin rashin tsaro da gazawar hukumomi a jihar wajen hana irin wannan ta’addanci.

By ukarofi