Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinan filaye da safayo, Dr Faisal Umar Kaita ya sanar da haka yace gwamnati ta riga ta sami fili mai tsawon hectre 100 a garin Gidan na Banje da ke ƙaramar hukumar.
Kwamishinan na magana ne a karin Ƙafur wajan bikin biyar diyya ga waɗanda aka karɓi filayen su domin gina kwalejin.
Ya bayyana cewa tuni gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da biyan Naira miliyan 270 matsayin diyya da aka biya masu filayen.
Manoma 241 aka biya diyya na filayen da aka amsa da kwamishinan ya danganta tsarin gwamnatin Dikko Raɗɗa na biyan diyya kafin fara aiki ga duk filin da gwamnati ta amsa.
Dr Faisal ya ce da zara an kammala aikin gina kwalejin zai zama wurin koyar da manoma jihar sabbin dabarun noma na zamani.
Kwamishinan ya yaba da ƙoƙari da Ibrahim Masari mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa kuma ɗan asalin karamar Ƙafur bisa ƙoƙarin da yayi na ganin an kawo kwalejin zuwa Ƙafur.
A jawabinsa Ɗangaladiman Katsina Hakimin Ƙafur Alhaji Abdulrahaman Abdullahi Rabe ya yabawa gwamnatin Dikko Raɗɗa bisa ƙoƙarin da tayi na biyan diyya ga manoman da aka amshi filayen su.
Ya ce wannan karamci da gwamnati tayi ta nuna ita mai tausayin al’ummar ta ne kuma zai taimaka wa mutanen su sake neman wani filin da zasu cigaba da noman su.
