Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
ƙungiyar Ci Gaban Garin Doho (DDA) a ƙaramar Hukumar Kwami, Jihar Gombe, ta karrama shugaban ƙaramar Hukuma, Dokta Ahmed Wali Doho, saboda jagorancinsa na shekaru guda da suka sauya rayuwar al’ummar yankin.
Bikin karramawar, wanda aka haɗa da taron addu’a da godiya, ya gudana ne domin nuna godiya ga irin jagorancin Dokta Wali, wanda aka bayyana a matsayin abin koyi da kuma mai cike da canje-canje na alheri.
Shugaban kwamitin shirya bikin, Farfesa Shu’aibu Umar Wazirin Doho, wanda kuma shi ne Pro-Chancellor na Jami’ar Benin, ya bayyana Dokta Wali a matsayin jagora wanda ya kafa sabon tarihi.
“Dokta Wali ya kafa sabon mizani na jagoranci ta hanyar kawo muhimman ayyukan da suka sauya rayuwar al’umma,” inji Farfesa Wazirin Doho.
Shi ma, Barista Sani A.A. Haruna, shugaban karamar hukumar Gombe kuma shugaban ALGON na Jihar Gombe, ya yaba da karramawar, yana mai cewa Dokta Wali ya cancanci wannan yabo.
“Nasarorin Dokta Wali suna bayyane, kuma suna nuna irin jajircewarsa wajen ci gaban al’umma
Wannan wani bangare ne na zabin gwamna Inuwa Yahaya na mutane masu kwarewa,” inji Barista Haruna.
Mai Shari’a Abdulhamid Yakubu Doho, alkali a babbar kotu kuma ɗan asalin yankin, ya yi kira ga al’ummar Doho da su ci gaba da goyon bayan Dokta Wali domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
A jawabinsa, Dokta Ahmed Wali Doho ya nuna matukar godiya ga al’ummar bisa wannan karramawa, yana mai cewa jagorancinsa ya dogara ne kan hidima da gaskiya.
“Ni dan hidima ne ga al’ummata. Wannan yabo zai kara karfafa min gwiwa wajen cigaba da aiki tukuru,” inji Dokta Wali.
Bayan haka, ya gode wa sauran shugabannin ƙananan hukumomi bisa hadin kai, tare da yaba wa ƙungiyar DDA da ta shirya taron ba tare da wani taimako daga gare shi ba.
An kuma gabatar da lacca kan jagoranci na gari da suka jaddada muhimmancin adalci da fifita jin dadin al’umma.
Malam Suleiman Tolba Magaji da Fasto Danjuma Maidugu ne suka gabatar da lakcar.
Taron ya kasance alama ta yabo da goyon bayan al’ummar Doho ga shugabancin Dokta Wali, tare da kira ga ci gaba da hada kai don cimma karin nasarori.
