Daga IBRAHIM MUHAMMAD
Ƙungiyar ’Yan Tifa da dangoginta na ƙasa, reshen jihar Kano ta yi kira ga Gwamnatin jihar Kano ta taimakawa yan ƙungiyar ta ba su motocin Tifa bashi a cikin sauwin kuɗi da za su riƙa biya a hankali hakan zai taimaka wajen bunƙasa harkokinsu da samawa matasa aiki.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa reshen jihar Kano, Kwamared Ibrahim Shafi’i Zainawa ya bayyana hakan da yake zantawa da ’yan jarida a wajen taron ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata.
Ya yi nuni da cewa idan aka yi la’akari da yadda Gwamnatin Abba mai albarka ta ke abubuwa na hangen nesa suna kira a tsaya suma a dubi lamarin su a sama musu motoci a matsayin na bashi yadda ake bai wa ƙungiyoyi na ’yan kasuwa a ɗora su akan layin da za su riƙa biya a hankali cikin sauƙi.
Da ya juya kan Ranar Ma’aikata ta Duniya da ake yace abin alfahari ne gare su sun kuma gamsu da yadda aka gudanar da taron na bana akan lokaci aka yi aka gama.
Ya ce, su a tsarin aikinsu a halin da ake ciki yanzu suna tafiya ne da yanayi da ake ciki na tsadar rayuwa suna ta ƙoƙari suma su ga sun sayar da kayan su cikin sauƙi yanda masu karamin ƙarfi za su yi amfani da kayan wajen gine-gine.
Ya ce suna alfahari da cewa mai sana’ar Tifa mutum ne da shi ɗaya yana samarwa mutane da yawa aikin yi a yau ɗin nan idan Tifa ta tsaya dabbar da take cikin gida a ɗaure sai ta san ta tsaya.
Ya ce yanzu suna fuskantar ƙalubale iri-iri musamman tsadar rayuwa abinda ka saba sayen sa N10,000 na kayan gyara a baya a yau in ka riƙe N50,000 ba zata saya maka wannan abin ba. Ba domin ƙalubale da ake fuskanta na tsadar kayan gyara a sana’ar Tifa ba da an sami sassauci wajen kayan gine-gine a birane da ƙauyuka.
Ya ƙara da cewa, a harkar kwashe shara da ake a jihar Kano a wurin mai Tifa ba ƙaramin abin alfahari ba ne don sharar ce ke toshe waɗansu magudanan ruwa da ke haifar da ambaliyar ruwa.
Kwamared Ibrahim Shafi’i Zainawa ya nemi Gwamnati ta kula ta sa ido akan harkar Tifa don basu gudummawa da ta dace musamman akwai wani gwanjon motoci da aka yi musu a Gwamnatin da ta wuce aka dan sami matsaloli duk da ana ta bibiyar abin Gwamnati tana iya ƙoƙarinta wajen yin bincike da ƙoƙarin samar da maslahar al’umma akan motocin.
