Manufarmu ita ce cusa ɗa’a da kishin ƙasa ga ’yan Arewa – AIRLIN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata ƙungiyar mai zaman kanta da ke wayar da kan al’ummar Arewacin Nijeriya kan muhimmanci yin zaɓe, cusa ɗa’a, nuna kishin ƙasa da kyautata tarbiyya mai suna ‘Adɓocacy for Integrity and Rule of Law Initiatiɓe’ (AIRLIN) ta yi kira ga ’yan Nijeriya musamman mazauna yankunan Arewa da su shiga cikin harkokin zaɓe ta hanyar amfani da ’yancin da tsarin mulki ya ba su da kuma zaɓen shugabanni nagari.

Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Muhammad Ibrahim Gamawa ya yi wannan kiran ne a yayin bikin ƙaddamar da ko’odinetocin jiha da ƙananan hukumomin Jihar Kaduna a Arewa House, ranar Talata.

Ya jaddada cewa, manufar ita ce a bai wa ’yan Nijeriya shawarar su kasance masu bin doka da oda, da mutunta juna ba tare da la’akari da bambancin addini da al’adu ba, yana mai cewa, kare martaba Nijeriya aiki ne da ya rataya a wuyan ’yan ƙasa, a ciki da wajen Nijeriya.

“Don haka ne ma muka zo nan domin aaddamar da ɗaya daga cikin ofisoshi 15 da muke da su a jihohin Arewa 19, domin burinmu shi ne mu mamaye dukkan jihohin Arewa, mun zo ne domin mu yi kira ga ‘yan ƙasa su zo su kaɗa auri’a a cibiyar da za su zaɓi shugabanni nagari.

“Idan za a iya tunawa a zaɓen da ya gabata, kashi 42 cikin 100 na masu kaɗa ƙuri’a ne kawai suka halarci wurarren zaɓe, 68 kuma ba su halarta ba wanda hakan ba shi da kyau ga ƙasar nan, don haka dole ne mu fito mu san waɗanda suka kasa zaɓe, mu fahimtar da su su zaɓi shugabanni da suka dace.

A wani ɓangare na manufofinsu na ƙara yawan masu kaɗa ƙuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, ƙungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan ƙasa wajen karɓar katin zaɓe, “Lokacin da INEC ta buɗe dandalin rajistar katin zaɓe, za mu taimaka musu wajen karɓar katin zaɓe domin su bada gudunmawa a zaɓe da kuma amfani da ’yancinsu.

Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama ɗan ƙasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi ƙaranci, abu ne mai sauƙi a laƙa wa ɗan Nijeriyar ba shi da katin ɗan ƙasa sharrin zama baƙo ko ɗan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane.

“Rashin katin shaidar zama ɗan ƙasa babbar matsala ce ga ’yan Nijeriya musamman waɗanda ke zuwa yankin Kudancin ƙasar nan.

“Amotekun ko wasu ƙungiyoyin al’adu ne za su tare su, za a tattara su a ce su bayyana kansu da kuma inda suka fito, wasu ma suna zargin su ba ’yan Nijeriya ba ne.

“Wasu za su ce ‘yan Kaduna ne amma ina katin shaida? Babu wata shaida ko da ta lasisin tuƙi ce.”

Ya kuma bayyana cewa, ƙungiyarsa na shirin gudanar da wani taro na kwana ɗaya domin karɓar baƙuncin Malamai aƙalla 200 a ƙaramar hukumar Gamawa waɗanda za su zo a wayar da kan jama’a game da gina ƙasa da haƙƙoƙin ‘yan ƙasa da ayyukansu sannan kuma su wayar da kan ɗalibai da ke ƙarƙashinsu.

A nasa jawabin, kodinetan AIRLIN na Jihar Kaduna Alhaji Musa Muhammed ya ce, ƙungiyar ta duƙufa wajen ganin ta kawo sauyi mai kyau da zai dawo da martaba da mutunta ‘yan Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, AIRLIN gida ce ga kowa da kowa musamman waɗanda suka yi imanin cewa akwai buƙatar a sake farfaɗo al’amuran da suka rushe a Nijeriya.

By ukarofi