Gwamnatin tarayya za ta gudanar da aikin hanyoyi biyar a Jihar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin tarayya za ta gina tare da kammala aikin wasu manyan hanyoyi a Jihar Katsina.

Sun haɗa da kammala aikin hanyar Katsina zuwa Kano da aka fara aikin faɗaɗa ta zuwa tagwayen hanya tun lokacin hawan mulkin Buhari amma akai watsi da hanyar bayan a ci kusan kashi hamsin da farawa.

Sai gyaran hanyar da ta taso daga Malumfashi zuwa Ƙafur ta isa zuwa Dabai da kuma Kano zuwa Kazaure ta miƙa zuwa Mai’adua.

Ƙaramin ministan ayyuka da gidaje Alhaji Muhammad Goranyo ya sanar da haka lokacin da ya kaiwa mataimakin gwamnan jihar malam Farouk Lawal Joɓe ziyara a ofishin sa.

Ya bayyana cewa shugaban ƙasa ne ya umurci ma’aikatan ziyarar gani da ido kan hanyoyin ƙasar da tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta fara ba ta kammala musamman a jihohin Arewa maso Yamma.

Ya ce gwamnatin tarayya ta tanadi isassun kuɗaɗen kammala aikin hanyoyin da gina sabbi tare da biyan diyya ga mutanen da za ayi amfani da filayen su wajan gina sabbin hanyoyin.

Ministan sai ya yi kira ga gwamnatin jihar da samar da cikakken tsaro ga ma’aikatan da za su gudanar da aikin hanyoyin a jihar.

A nasa jawabin mataimakin gwamnan jihar Malam Farouk Lawal Joɓe ya nuna jin daɗin sa ga yadda gwamnatin tarayya ta waiwayi aikin waɗannan hanyoyi musamman hanyar Katsina zuwa Kano da ya ce zai bunƙasa tattalin arzikin jihar da kuma inganta tsaro da zaran an kammala aikin.

Ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na bada gudummawar duk abinda ya kamata domin kammala aikin hanyoyin kan lokacin da aka tsara.

Haka kuma Malam Farouk Joɓe ya tabbatar wa ministan cewa gwamnatin jihar Katsina a shirye take ta bada cikakken tsaro ga masu aikin hanyar da kula da kayan aikin.