Tinubu ya amince da bayar da tallafin 50,000 ga magidanta 100,000 na tsawon watanni uku

Spread the love

Daga KHADIJA ABUBAKAR

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da shirin gina ƙasa da tallafawa magidanta a yayin wani zama da Majilisar kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasa, NEC a Abuja.

Wani jawabi da ya fito daga ofishin mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya ce manufar shirin su ne dan a inganta harkokin noma da tattalin arziƙi gami da bada tallafi domin rage raɗaɗin talauci ga ƴan Najeriya.

Shirin wanda ya samu goyon bayan Majalisar ta NEC, ya ƙunshi rarraba kuɗaɗe da yin ayyukan more rayuwa a dukkan shiyyoyin ƙasarnan guda shida, inda za a bada tallafin Naira 50,000 ga iyalai 100,000 a kowace Jiha na tsawon watanni uku.

Ya ƙara da cewa gwamnatin ta kuma ware Naira biliyan ɗari da hamsin da biyar domin sayan kayan abinci da kuma raba su ga magidanta don samun sauki ta fuskar mallakar abinci a cikin al’umma.

Ngelale ya ce, shugaba Tinubu ya yi kira ga gwamnoni da su bada haɗin kai wajen ganin sun samar da buƙatun al’ummarsu da kuma inganta harkokin noma.

By Babaji