Shugaban hukumar EFCC Mr Ola Olukoyede, ya umarci da a kama jami’an hukumar waɗanda suka faɗa otal a Legas.
A wani faifan bidiyo, an nuna wasu jami’an EFCC din sun kutsa kai cikin wani ɗakin otal inda suka mari wata mata da tace ma’aikaciya ce a otal din. Duk abinda ya faru wata kyamaran CCTV dake otal din ta naɗa.
Shugaban hukumar ya cigaba da cewa atisayen ranar, ya faru da safiya sannan sunyi nasarar cafke masu laifi da dama. Yace kuma jami’an sa da suka wuce gona da iri, za ai bincike mai zurfi domin hukunta su.
