Gwamnoni sun kira taron gaggawa kan batun mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata

Spread the love

Daga Farouk Abbas

Gwamnonin Jahohi 36 na ƙasarnan zasu gudanar da taron gaggawa a yau, Laraba kan batun sabon mafi ƙarancin albashi da za a ke biyan ma’aikata a Najeriya.

A kwanakin baya ne gwamnonin suka ƙi amincewa da tayin dubu 62 da gwamnatin tarayya ta yi inda suka ce amincewa da hakan zai sa sai wasu gwamnonin sun ciyo bashi kafin su iya biya.

Sai dai ita kuma haɗaɗdiyar ƙungiyar ƙwadago tana kan bakanta na buƙatar ake biyan naira dubu 250.

Taron gwamnonin na zuwa ne sakamakon ficewa daga batun da majalisar ministoci ta shelanta a jiya inda ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Idris Mohammed ya ce sun yi hakan ne ganin yadda batun ya ƙunshi ƙananan hukumomi, da jihohi, da gwamnatin tarayya da kuma haɗaɗɗiyar kungiyar ƙwadago.

Halima Ahmed, wacce ita ce daraktar wucin-gadi na yaɗa labarai ga ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta sanar da jaridar ‘Daily Trust’ cewa za a yi taron ne da misalin ƙarfe 7 na dare kan batun a Abuja.

By Babaji