Salman Dogo ya kama aiki a matsayin sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano a matsayin kwamishina na 46 ga jihar.
An haife shi 21 ga watan Yuli 1966 a Illorin, jihar Kwara. Salman Dogo ya fi shekara 30 da shiga aikin ɗan sanda.
Salman Dogo ya shiga aikin ɗan sanda a shekarar 1992, ya riƙe mukamai da dama a ƙasar nan kamar jagorancin sashen da ke kula fashi da makami na rundunar yan sanda wanda ake kira “Anti robbery squad”. Ya taɓa rike muƙamin Area Commander a jihohin Legas, Kaduna da kano. Yayi mataimakin kwamishina a jihar Anambra da Bauchi.
A na fatan ƙwarewar sa zai taimaka wajen tsaron jihar kano sosai.