“Burina na kafa gidauniya don taimaka wa mata”
Daga ABUBAKAR A. BOLARI, a Gombe
Hajiya Laure Umaru Masokano, tsohuwar malamar makaranta ce a garin Nguru ta Jihar Yobe a Arewa maso gabas na tarayyar Nijeriya kuma ‘yar kasuwa, gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati wacce ta yi ilimin ta a ɓangaren ilimin shari’a da na arabiya, wato Islamic studies. A zantawarta da shafin Gimbiya na jaridar Manhaja, ta bayyana tarihin rayuwar ta da ma wasu ɓangarori daban. Ku biyo mu ku sha karatu:
MANHAJA: Za mu so ki gabar da kanki ga masu karatunmu.
HAJIYA LAURE: Sunana Hajiya Laure Umaru Masokano ni haifaffiyar garin Nguru ce Arewa maso gabashin tarayyar Najeriya daga Jihar Yobe, anan garin Nguru aka haife ni a ranar 1 ga watan Yuli a shekara ta 1983. Na shiga makarantar firamare a firamare ta Hausari a shekarar 1988, na gama a shekarar 1993, sannan na tafi makarantar sakandare ta Army Day Secondary School Nguru daga shekarar ta 1993 na kammala a shekarar 1999. Ina gama sakandare sai aka min aure. Bayan na yi aure ne na tafi na yi difloma a ɓangaren shari’a tsakanin shekara ta 2004 zuwa 2006, ina gamawa a shekara ta 2008 zuwa 2013 na tafi na yi digiri ɗina na farko a ɓangaren Islamic Studies a Jami’ar Maiduguri.
Me aka sa a gaba, aiki ne ko sana’a?
Eh ina aikin gwamnati na fara aiki ne a lokacin da na gama karatun sakandare inda na fara aikin koyarwa a firamare ta Inglewa da ke a garin na Nguru, a lokacin da na yi aure sai na bar koyarwa na koma Abuja, ina nan bana aikin komai har sai da na gama digiri ɗina a jami’a inda yanzu nake aiki a National Board For Arabic and Islamic Studies (NBAIS) a Jihar Kano.
Rayuwa cike take da ƙalubale, ko kin fuskanci wasu ƙalubale a tafiyar ki?
Gaskiya dai a yanzu ban fuskanci kowanne irin ƙalubale ba, amma dai na san aikin gwamnati akwai ƙalubale a cikin sa musamman ma ga ‘Ya Mace da take aiki a tsakanin Mazaje wacce ba kowanne Namiji bane yake son ganin ci gaban Mace a wajen aiki ba.
Za mu so jin irin nasarorin da ki ka samu.
Alhamdulillahi babban nasarar da na samu a rayuwa ita ce yadda na samu aiki nake yi nake dogaro da kai na ba tare da na zamewa mutane matsala ko na ɗaura musu wata ɗawainiya ba kuma in sha Allah wannan aiki zai kai ni inda ban yi tsammani ba a rayuwa.
Wace irin shiga ki ka fi sha’awar yi?
A matsayi ta ta Bahaushiya kuma ‘yar Arewa na fi son na sanya doguwar riga ta atamfa wacce ba ta matse ni ba wanda ko’ina zan iya shiga ba wanda zai ce min na yi shigar da ba ta dace ba kuma za a min kallon mutunci da kamala.
Wane irin abinci ki ka fi so?
Na fi sha’awar tuwo da miyar ganye ko kuma shinkafa da wake da mai da yaji ko kuma da miya.
Ko akwai wata ƙungiya da ki ke ciki?
Ni mamba ce a ƙungiyoyi da dama tun ina sakandare har na shiga jami’a, yanzu haka ma ina cikin wata ƙungiya ta Aspire Women Forum Yobe State.
Za mu so jin ƙasashen da ki ka taɓa ziyarta.
Na je Ƙasar Saudi Arebiya na kuma je Ƙasar Daular Larabawa UAE Dubai harkar kasuwanci domin ni yar kasuwa ce.
Akwai iyali ko babu?
Alhamdullah ina da yara guda biyar. Namiji ɗaya da mata huɗu kuma dukkan su suna raye.
Wane buri ki ke da shi a rayuwa?
A Rayuwata ba ni da wani burin da ya wuce naga na kafa wata gidauniya ta ƙashin kaina da zan yi amfani da ita wajen taimakon mata da ƙananan yara musamman don share musu hawaye a ɓangarorin rayuwa daban daban.
A matsayinki ta ‘ya mace wacce shawara za ki ba wa mata?
A matsayi na ta ‘ya mace ina mai amfani da wannan damar ina bai wa iyaye shawara da mu yi ƙoƙarin mu tsaya wa yaran mu mata su yi karatun zamani na boko gami da na addini saboda karatun ‘ya mace a wani lokaci ya fi na ɗa namiji muhimmanci sosai domin duk macen da take da ilimi yanayin rayuwarta ma daban ne da na wacce ba ta da ilimi ba idan aka ilimantar da ‘ya mace bakiɗaya al’umma aka ilimantar domin ita uwa makaranta ce ta farko wacce take fara kula da tarbiyar ‘ya’yanta tun daga gida don a gaskiya a zamantakewa na rayuwa idan ka haɗa makwabtaka da jahilar mace masifa ne ballanta ma ace zaka aure ta har ku samu iyali da ita. Saboda haka yana da mahimmaci mu ilimantar da yaranmu mata idan mu ka yi hakan lalle muntaimaki kanmu muntamaki ita yarinyar da kuma duk wanda zai aure ta.
Mun gode.
Ni ma na gode.

