Mawaƙi Rema ya kafa tarihi a duniyar waƙa

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Mawaƙi Rema ya kafa tarihi a duniyar waƙoƙi ko in ce a mawaƙan Afrika, inda waƙarsa ta ‘Baby Calm Down’ ta zama waƙar Afirka da aka fi sauraro a Amurka.

Waƙar Calm Down ta mawaƙin Najeriya, Rema ta ci gaba da kafa tarihi, inda ta zamo ta ɗaya a cikin waƙoƙin ƴan Afirka (Afrobeats) da aka fi sauraro a Amurka.

Haka nan ta zamo waƙar ƴan Afirka ta farko a tarihi da aka saurara sama da sau biliyan ɗaya a Amurka, kamar yadda shafin lura da waƙoƙi na Chart Data ya bayyana a shafinsa na X.

Ko a bara, Chart Data ya bayyana waƙar ta Calm Down a matsayin waƙar ɗan Afrika da ta fi samun nasara a tarihi.

An bayyana cewa sirrin nasarar waƙar ya samu ne daga yadda aka rera ta cikin natsuwa da yanayi mai kwantar da hankalin mai sauraro.

“Hakan kan sanya waƙa ta shiga tare da zama a cikin tunanin mai sauraro ta yadda zai so ya sake sauraron ta,”inji Chart Data. 

A watan Fabarairun 2022 ne aka saki waƙar, a cikin wani kundin waƙoƙi na mawaƙin.

Watanni kaɗan bayan hakan, Rema, wanda asalin sunansa shi ne Divine Ikubor ya haɗa gwiwa da mawaƙiya Selena Gomez domin sake inganta waƙar, wadda aka saurara sau biliyan ɗaya a manhajar sauraron waƙ oƙ i ta Spotify.

Waƙ ar ta sanya Rema ya shiga cikin sahun shahararrun mawaƙan Najeriya irin su Burna Boy da Wizkid da kuma Davido.

By ukarofi