Abdulkareem zai isa Ƙasar Lithuania don halartar bita kan hana cin hanci

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Ƙwararren mai shirya finanninai, kuma mai kula da shirye-shirye a kampanin moving image limited, mazaunin Kano, Abdulkareem Mohammed zai wuce Ƙasar Lithuania don halartar bita ta ƙasa da ƙasa kan hana cin hanci (IACC)  na 2024.

Yayin magana da Nigerian Kicker ranar Juma’a a ofishinshi da ke cikin garin Kano, Mohammed, wanda ake sa ran zai bar Nijeriya a ranar Asabar ya bayyana cewa, aƙalla ana tsammanin mutane 1000 zasu halarci wannan taro daga ƙasashe 120.

Ana sa ran zai yi sharhi mai taken Yammacin Labarai: Magance Rashawa Ta Hanyar Hakokkki a sahen su na yamma wanda MacArthur Foundation suka shirya.

Daga cikin abubuwan da sharhin ya ƙunsa, zasu nuna jajircewarsu don ƙarfafa wannan ɗaukin na MacArthur Foundation, karɓuwar alumma da tasyin dakan akan yaƙi da rashawa.

A cewar wani yanki na sharhin, “Tallafin da MacArthur foundation suka bamu ya buɗa hanyar magance canjin ɗabi’u ta hanyar shirin wasan kwaikwayo mai suna ‘Shugabanci’ da ake gabartwa a radiyo da harshen Hausa. Wannan shirin na ƙarfafa ɗaukar nauyi/hakki da kowa da ruwanka a haifaffun yan Arewacin Nijeriya, sannan ya ƙarfafa wannan ɗaukin na MacArthur Foundation, karbuwar alumma da tasirin su kan yaƙi da rashawa.

“Baya ga wannan yana kuma haɗawa da ƙorafe-ƙorafen alumma da kuma muryoyinsu.”

Moving image limited kaga ce ta sadarwar da ke yaɗa shirya-shiryenta ta hanyar rediyo da talabijin da kuma fitar da finafinai.

Kamfanin ya samar da aikin yi ga ƙungiyoyi, jihohi da ma ƙasa bakiɗaya a tsayin shekaru 30 da kafuwar shi.

Haka kuma sun zama kamfanin da ya shirya talla ta radiyo da talabijin wadda Babban Bankin Nijeriya, ta ɗauki nauyi, wadda ke lurar da ‘yan Nijeriya zuwa ga hanyar da gwanmatin tarayya ta gabatar don bunƙasa noma da kiwo.

Moving Image is currently handling a six-year (2018 – 2024) Hausa Radio drama series on anti-corruption campaign funded by MacArthur Foundation.

Yanzu haka kamfanin na yin shirin wasan kwaikwayo na tsawon shekaru shida, daga shekara ta 2018 zuwa shekara ta 2024, kuma shirin na radiyo ne da ake yi a harshen Hausa wanda MacArthur foundation suka ɗau nauyi dan magance rashawa kamar yadda muka ambata.

By ukarofi