Daga CMG HAUSA
Yau Talata, 27 ga wata sashen kandagarkin kutsen na’ura mai ƙwaƙwalwa na ƙasar Sin ko CVERC a taƙaice da kamfanin fasaha na Qihoo 360 sun ƙaddamar da rahoton bincike na biyu dangane da yadda aka yi kutse a na’urori masu ƙwaƙwalwa na jami’ar koyar da ilimin fasaha ta ƙasar Sin, ko Northwestern Polytechnical University, inda aka yi ƙarin bayani kan yadda hukumar leƙen asiri ta Amurka ko NSA, ta yi amfani da wata kafa mai laƙabin TAO wajen yin kutsen fiye da sau dubu guda.
Ta haka an ƙara sanin yadda NSA take satar bayanai a yanar gizo.
Gwano ba ya jin warin jikinsa. Ƙasar Amurka ba za ta iya musunta abin da ta aikata ba.
Haƙiƙa dai Amurka ta daɗe tana satar bayanai a yanar gizo a fili.
Edward Snowden, tsohon ma’aikacin kamfanin da ya daddale kwangila da gwamnatin Amurka ya bayyana wa kafofin yaɗa labaru a shekarar 2013 cewa, NSA tana leƙen asiri a duk fadin duniya a ko da yaushe.
Rahoton da wani kamfanin yanar gizo na ƙasar Sin ya gabatar a bana ya nuna cewa, a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, NSA ta yi kutse a na’urori masu ƙwaƙwalwa a wurare 403 da ke ƙasashe da yankuna 47 a duniya, ciki har da ƙasashen Sin, Birtaniya, Jamsu da Faransa.
Yayin da Amurka take satar bayanai bisa ga fasahar zamani, tana kuma mayar da kanta wadda aka yi wa kutsen, har ma ta haɗa hannu da kawayenta don shafa wa ƙasar Sin baƙin fenti.
Rahotannin ƙasar Sin sun taimaka wa ƙasashen duniya ƙara sanin gaskiyar lamarin.
Mai fassara: Tasallah Yuan
