Kamfanin Sin Na taimaka wajen gina “Kusurwar Ƙasar Sin” a Abujan Najeriya

Daga CMG HAUSA

An gudanar da bikin bude “Kusurwar ƙasar Sin” a makarantar gwamnati dake gunduma ta 11 a birnin Abuja, fadar mulkin tarayyar Najeriya, wanda rukunin kamfanin CRCC na ƙasar Sin reshen Najeriya ya gyara a safiyar ranar 23 ga wata.

Bikin ya samu halartar ƙaramin jakadan ƙasar Sin dake Najeriya Zhang Yi, da darektan cibiyar yaɗa al’adun ƙasar Sin a ƙasar Li Xuda, da manajan kamfanin CRCC reshen Najeriya Wan Lianyu, da shugaban hukumar ba da ilmi a matakin farko ta birnin Abuja Alhassan Sule, da wakilan ƙungiyar malamai da ɗalibai na makarantar da wasu manema labarai.

A jawabinsa yayin bikin, karamin jakadan ƙasar Sin dake Najeriya Zhang Yi ya bayyana cewa, aikin ba da ilmi shi ne tushen ci gaban ƙasa, don haka, ofishin jakadancin ƙasar Sin yana ba da muhimmanci ga cuɗanyar ba da ilmi dake tsakanin Sin da Najeriya, haka kuma ya daɗe yana haɗa kai tare da kamfanonin ƙasar Sin dake Najeriya, domin raya aikin ba da ilmi a ƙasar.

A nasa ɓangare, shugaban hukumar ba da ilmi a matakin farko ta birnin Abuja Alhassan Sule, ya gode wa ofishin jakadancin ƙasar Sin da kamfanonin kasar Sin dake Najeriya, bisa ƙoƙarinsu na inganta yanayin makarantun ƙasar, da samar da tallafin kuɗi ga ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi.

Haka kuma ya yaba da aikin gyara makaranta da kamfanonin ƙasar Sin suke yi.

Yana mai cewa, nan gaba makarantar za ta kare sabbin kayayaykin da aka samar musu, tare kuma da yada al’adun ƙasar Sin a ƙasar yadda ya kamata.

Mai fassarawa: Jamila