An kuɓutar da mutum bakwai daga hannun ’yan bindiga a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar Tsaro sun kuɓutar da wata uwa da ’ya’yanta uku da wasu ƙarin mutum uku daga hannun ’yan bindiga a Jihar Kaduna.

Dakarun Tsaro na ‘Operation Forest Sanity’ sun yi nasarar kuɓutar da mutanen bakwai ne yayin wani aikin sintiri a tsakanin yankunan Birnin Gwari zuwa Chikun.

Wannan dai na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamshinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na Tiwita.

A cewarsa, Gwamnatin Kaduna wadda ta yaba wa ƙwazon dakarun, tuni ta damƙa mutanen hannun makusantansu.

Sameul Aruwan ya ce, dakarun tsaron sun yi nasarar kuɓutar da mutanen ne lokacin da suke sintiri a kan titin Birnin Gwari zuwa Gayam zuwa Kuriga zuwa Manini.

Ya ce ’yan bindigar sun buɗe musu wuta, inda su kuma suka mayar da martani nan ta ke tare da murƙushe maharan, waɗanda suka tsere cikin daji.