Kusan ƙasashe 70 sun nuna rashin amincewarsu da tsoma baki a harkokin cikin gidan Ƙasar Sin

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Wasu rukunin ƙasashe sun jaddada rashin amincewarsu, a yayin zaman kwamitin kare haƙƙin ɗan-Adam na MƊD karo na 51 da yanzu haka ke gudana a birnin Vienna, kan yadda wasu ƙasashe ke tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar Sin.

Suna masu cewa, batutuwan da suka shafi Xinjiang, da Hong Kong da Tibet, harkokin cikin gida ne na ƙasar Sin, kuma bai kamata a riƙa siyasantar da batun haƙƙin ɗan Adam da nuna ma’aunai biyu ko tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar Sin ta hanyar fakewa da batun kare haƙƙin ɗan Adam ba.

Wata sanarwar haɗin gwiwa da ƙasar Pakistan ta gabatar a madadin ƙasashe 68, ta jaddada cewa, mutunta ikon mulki, da ‘yancin kai da cikakkun yankuna da rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na ƙasashe masu cin gashin kansu, na wakiltar muhimman ƙa’idojin da suka shafi dangantakar ƙasa da ƙasa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ya kamata dukkan ɓangarori, su martaba manufofi da ƙa’idojin yarjejeniyar MƊD, da kiyaye ƙa’idojin ƙasa da ƙasa, da rashin nuna son kai, da nuna gaskiya da adalci, da mutunta ‘yancin jama’ar kowace ƙasa na zabar hanyar samun ci gaba daidai da yanayin ƙasashensu.

Ta ƙara da cewa, ya kamata a kula da dukkan haƙƙoƙin bil-adama ba tare da nuna bambanci ba, da ba muhimmanci ga ‘yancin tattalin arziki, da zamantakewa da al’adu da kuma musamman ‘yancin ci gaba.

Mai fassara: Ibrahim

By Editor