
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alhinin rashin ɗaya daga cikin fitattun tsofaffin jaruman Kannywood, Abdullahi Shu’aibu, wanda aka fi sani da Karƙuzu.
Marigayin, mai shekaru 94 a duniya, ya rasu ne kwanaki kaɗan da suka gabata bayan fama da rashin lafiya.
A wata sanarwa da Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a ranar Juma’a, gwamnan ya ce mutuwar Karƙuzu ta haifar da babban giɓi a masana’antar Kannywood da ka iya wahalar maye gurbinsa, ya na mai cewa ya kasance wanda ya ke bai wa taurari da dama horo a matsayin sa na wanda ya ƙware a harkokin wasan kwaikwayo.
Ya ce, a madadin Gwamnatin jihar da al’ummarta, suna miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin da Kannywood da masana’antar finafinai baki ɗaya.
Ya kuma yi masa fatan samun rahamar Allah SWT da kuma shiga aljannar Firdausi.
