A ranar Juma’a, wata girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta kai girman 7.7 a ma’aunin Richter ta afku a tsakiyar ƙasar Myanmar, kamar yadda yukumar bincike ta Ƙasa da Ƙasa (USGS) ta bayyana. Girgizar ta haddasa lalacewar hanyoyi a babban birnin ƙasar, Naypyidaw, tare da jin tasirinta a ƙasashen China da Thailand.
Rahotanni sun nuna cewa cibiyar girgizar ƙasar tana nisan kilomita 16 daga arewa maso yammacin birnin Sagaing, a zurfin kilomita 10 daga ƙasa, kuma ta afku da misalin ƙarfe 12:50 na rana agogon yankin (0620 GMT).
A Bangkok, an dakatar da wasu hanyoyin jirgin ƙasa na ƙarƙashin ƙasa da na sama sakamakon girgizar ƙasar.
Shaidun gani da ido sun ce girgizar ta janyo faɗuwar ginin, tare da fashewar wasu hanyoyi a Naypyidaw.
Haka kuma, an ji tasirin girgizar a Arewacin Thailand har zuwa babban birnin ƙasar, Bangkok, inda mutane suka ruga zuwa tituna saboda girgizar. Wata mazauniya birnin Chiang Mai, mai suna Duangjai, ta shaida wa AFP cewa: “Na ji ƙarar girgizar lokacin da nake barci a cikin gida, sai na ruga na fita da gudu a cikin kayan barci na.”
A ƙasar China, hukumar kula da girgizar ƙasa ta Beijing ta bayyana cewa an ji tasirin girgizar a lardin Yunnan, kuma ta yi ƙarfinsa zuwa 7.9 a ma’aunin Richter.
A baya, girgizar ƙasa mai ƙarfi na faruwa a Myanmar, musamman a yankin fault line na Sagaing, inda aka samu girgizar ƙasa mai girman 7.0 ko fiye har sau shida tsakanin shekarun 1930 zuwa 1956. A shekara ta 2016, wata girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta kai 6.8 a garin Bagan ta hallaka mutane uku, tare da rushewar wasu gine-ginen tarihi.
Kasancewar Myanmar ƙasa ce da ke fama da matsalar karancin kayayyakin lafiya, ana fargabar cewa girgizar ƙasar na iya jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali, musamman a yankunan karkara.
