
Daga BELLO A. BABAJI
Aƙalla mutane 144 ne suka rasa rayukansu tare da wasu 732 da suka samu raunuka a yayin da wata girgizar ƙasa da ta auku a yankin Myanmar dake kusa da ƙasar Thailand, ranar Juma’a, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.
Gwamnatin ta ce, lamarin ya haifar da rushewar gidaje da wasu gine-gine na faɗin ɗaruruwan mila-milai.
Tun bayan aukuwar lamarin ne ake ƙoƙarin gano adadin mutanen da suka rasa rayukansu da waɗanda suka samu raunuka musamman a Myanmar, wadda ɗaya ce daga cikin ƙasashe marasa ƙarfi a duniya.
Tuni dai gwamnatin ƙasar ta sanar da sanya dokar ta-ɓaci a babban birninta da birni na biyu mafi girma a ƙasar. Haka ma a Bangkok ta ƙasar Thailand.
Ana ganin akwai yiwuwar adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya ƙaru kasancewar ana cigaba da gano wasu gawawwaki.
